Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta cafke daraktan kudi da asusu na hukumar bunkasa shiyyar Niger Delta (NDDC), Eno Ubi Otu bisa zarginsa da shiga a dama da shi wajen almundaha da sama da fadi na naira biliyan 25.
Wata majiya mai tushe ce ta tabbatar da hakan ga jaridar LEADERSHIP a daren ranar Laraba, ta na mai cewa Otu dai ya fada komar EFCC ne bisa kes din da ya shafi zargin karkatar da sama da kudaden haraji na fiye da biliyan 25.
Otu, wanda ya je ofishin EFCC tun da safiyar ranar Laraba domin amsa wasu tambayoyi amma har zuwa lokacin hada wannan labarin na cigaba da fuskantar tambayoyin kan wannan batun.
Majiyar ta kara da cewa kamen na zuwa domin zurfafa bincike kan rahoton binciken kudade na hukumar ta NDDC.
Da jaridar LEADERSHIP ta yi kokarin jin ta bakin kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren domin neman tabbacin ko karin haske daga bakinsa ba a iya samunsa ba.