Hukumar da ke kula da jami’an tsaron Civil Defence, jami’an tsaron gidan yari, jami’an ‘yan kwana-kwana da na hukumar kula da shige da fice (CCFIB), ta amince da yin karin girma ga jami’an hukumar kashe gobara na tarayya (FFS) su 2,382.
Kakakin hukumar kashe gobara ta tarayya FFS, ACF Paul Abraham, shine ya sanar da hakan ta cikin sanarwar da ya fitar wa manema labarai a ranar Laraba.
Acewar sanarwar, Kwanturola Janaral na FFS, Injiniya Jaji Abdulganiyu shine ya sanar da karin girma da cigaban a wata takardar cikin gida da ya fitar.
Ya ce manyan jami’ai 363 ne karin girman ya shafa, yayin da kuma 2,019 suka kasance masu dafa wa Sufuritendan (ASF I) da mataimakan sufuritandan (DSF) da suka samu cigaba a shekarar 2022.
Jaji ya jinjina wa ministan kula da harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, da shugaban hukumar CCFIB hadi da sauran wadanda suka taka rawa wajen kara wa jami’an sa girma.
Sai ya taya daukacin jami’an da karin girma da cigaban ya shafa tare da jawo hankalinsu da su kara himma da kwazo domin tabbatar da karin girma da aka musu sun cancanta.
Jaji ya umarci shugabannin hukumar a rassan kasar nan da su sanya wa jami’an da karin girman ya shafa shaidar karin girman nasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp