A ranar 6 ga wata ne aka kaddamar da wani taro na tsawon kwanaki 15 tsakanin Sin da kasar Senegal, domin ba da horo kan cikakken tsarin masana’antar gyada, wanda ya tattaro mahalarta 14 daga kasar Senegal, wadanda suka hada da masu bincike, da jami’an gwamnati da kuma ‘yan kasuwa.
Aikin gona wani gagarumin bangare ne cikin tattalin arzikin kasar Senegal, inda noman gyada ya kasance muhimmiyar hanyar samar da kudin shiga da aikin yi, Sai dai kamar yadda muka sani, har yanzu kasashen Afrika ne koma baya a bangaren amfani da fasahohin zamani a ayyukan gona da masana’antu, wadanda ake matukar bukata domin samun ci gaba.
- Sin Da Masar Za Su Karfafa Dangantakarsu Karkashin Kungiyar SCO
- Adadin Masu Amfani Da Intanet A Sin Ya Kai Sama Da Mutane Biliyan 1.12
Idan muka kwatanta su da Sin, za mu ga wagegen gibin dake akwai tsakanisu a wannan bangare. Kasar Sin ba ta da arzikin filin noma kamar kasashen Afrika, amma tana iya dogaro da abun da take samu wajen ciyar da al’ummarta, sabanin kasashen Afrika da har yanzu suke fama da matsalar yunwa saboda rashin wadatar abinci.
Mene ne dalilin bambancin dake tsakanin bangarorin biyu? Kasancewarta jajirtacciya, kasar Sin ta yi kokarin lalubo hanyoyin ciyar da kanta ta hanyar amfani da fasahohi da sabbin dabarun raya aikin gona. Irin wannan basira da gogewa ta kasar Sin, kasashen Afrika suke bukata muddun suna neman zama masu dogaro da kansu.
Karin maganar Sinawa dake cewa, ka koya wa mutum su maimakon ba shi kifi abu ne da muka gani a zahiri. Misali shi ne yadda a ko da yaushe wasu kan yi amfani da tallafin kudi da suke bayarwa wajen yin barazana da shiga harkokin gidan ’yantattun kasashe da yadda hakan ke haifar da koma baya da jefa kasashen da suka dogara da tallafi cikin mummunan yanayi.
Na san zuwa yanzu kowa zai amince cewa, kasar Sin ta bullo da sabuwar dabara ta abota da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da ya bambanta da ta masu son cin zali da neman iko. Koyar da fasahohin da za su taimakawa kasashe masu tasowa musamman kasashen Afrika, zai kai su ga habaka ayyukansu da samar da sabbin dabarun ci gaba ta yadda za su habaka noma a cikin gida da sarrafa albarkatu har ma da shigar da su kasuwannin duniya. Wannan zai kai su ga samun wadata da ba su damar tsayawa da kafarsu. Tabbas wannan ya nuna cewa, kasar Sin aminiya ce ta kwarai mai son ganin dorewar ci gaban kasashe maimakon amfani domin mayar da su masu amshin shata, lamarin da zai kai ga cimma burin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp