Tsohon ɗan majalisar wakilai, Tajudeen Yusuf, ya gargaɗi jam’iyyar PDP da ta bai wa yankin Kudu tikitin takarar shugaban ƙasa na 2027 ko kuma ta fuskanci matsala.
Ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, inda ya buƙaci jam’iyyar da ta yi abin da ya dace domin dawo da goyon bayan jama’a a faɗin ƙasar.
- Wang Yi Ya Gabatar Da Jawabi Albarkacin “Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kan Kasa Da Kasa” Karo Na Farko Na MDD
- Xi Ya Zanta Da Takwaransa Na Kasar Koriya Ta Kudu
Yusuf, wanda ke daga cikin na hannun damar Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya, ya ce, bai wa Kudu tikitin zai iya janyo fitattun ‘yan siyasa kamar Peter Obi na jam’iyyar Labour Party su dawo cikin PDP.
Ya ce dawowar Obi cikin jam’iyyar zai ƙara mata ƙarfi, saɓanin abin da ya faru a 2023 lokacin da rashin daidaito wajen rabon tikiti ya sa Obi ya bar jam’iyyar.
“Da Obi ya tsaya tare da Atiku kuma aka zaɓe shi mataimaki, da PDP ta ci zaɓen,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe zaɓe shi kaɗai.
“Ku bai wa Kudu tikitin, ku ga sakamako. Amma idan PDP ta ci gaba da tafiya a kan wannan kuskure, to, za ta fuskanci babbar matsala a 2027,” Yusuf ya bayyana.
Ya kuma bayyana cewa Atiku Abubakar ba ɗa jam’iyyar PDP ba ne a yanzu, yana tare da wata sabuwar tafiyar haɗin gwiwa ta siyasa.
Yusuf ya ɗora alhakin faɗuwar jam’iyyar a zaɓen 2023 kan rashin kyakkyawan shugabanci da kuma rabon tikiti ba bisa ƙa’ida ba.
Ya ce rikicin cikin gida da kuma gazawar PDP wajen kulawa da ‘yan Kudu ne suka sa jam’iyyar ta faɗi.
Ya kuma nuna takaicinsa game da sauya sheƙar Gwamnan Jihar Delta na baya, Ifeanyi Okowa, zuwa jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan na nuna cewa PDP ta kasa tsara kamfen ɗinta yadda ya dace.
Ya buƙaci shugabannin PDP da su daina dogaro da tsofaffi a siyasa, su mayar da hankali wajen gina sabuwar amana da haɗin kai, musamman a yankin Kudu.
A cewarsa, adalci, haɗin gwiwa, da sake gina jam’iyya su ne kawai hanyar da PDP za ta iya dawowa da ƙarfi a zaɓen 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp