Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi suka kan kisan gillar da aka yi wa Aishatu Abdullahi mai shekara 58, mai ‘ya’ya takwas a unguwar Jekadafari da ke cikin garin Gombe, inda ya bayyana lamarin a matsayin na rashin imani.
Gwamnan ya umarci ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa da su kaddamar da bincike tare da tabbatar da an gurfanar da wadanda suka aikata wannan danyen aiki a gaban kuliya.
- Abin Da Ya Sa Muka Sa Takin Zamani Cikin Tallafin Jama’a – Gwamnan Filato
- Messi Zai Iya Lashe Kyautar Ballon D’or Ta Bana
Ya sha alwashin cewa Jihar a karkashin jagorancinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron al’ummar jihar, kamar yadda Ismaila Uba Misilli Babban Darakta Yada labarun gwamnan jihar ya nakalto ta cikin wata sanarwar.
“Ba za mu taba lamuntar aikata laifuka ba, kuma wannan lamarin zai kara karfafa aniyarmu na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jiharmu”.
“Ina bayyanawa cewa wadanda suka aikata wannar aika-aikar ba za su sha ba har sai sun fuskanci shari’a, mun umurci jami’an tsaro su bi diddigin waɗanda suka aikata wannan aika-aika domin su girbi sakamakon mugun aikin da suka aikata.
Ya mika jaje ta ta’aziyyar gwamnati da al’ummar Jihar Gombe ga iyalan marigayiyar.
“Bayanin wannan lamari kamar yadda ‘yan sanda suka bayar tun farko, wani abu ba ne mai ban tsoro da takaici. Zukatanmu sun kadu tare da tausayawa iyalan wacce ta rasa ranta, wadanda suke cikin jimami maras misaltuwa, da kuma al’ummar Jekadafari da ma dokacin al’ummar Jihar Gombe, waɗanda suke cikin takaici sakamakon wannan mummunan lamari.”
Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar su kwantar da hankalinsu su kuma sanya ido don magance duk wata barazanar tsaro, yana mai alƙawarin cewa Jihar Gombe ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin da take da su.