Tsohon dan wasan Manchester United, Sir Bobby Charlton, ya mutu yana da shekara 86 a duniya.
Charlton ya taka rawar gani a gasar Kofin Duniya a 1966 da Ingila ta kartbi bakunci kuma ta lashe bayan doke kasar Jamus.
- A Bankado Wadanda Suka Kashe Dattijuwa – Gwamnan Gombe Ga Jami’an Tsaro
- Messi Zai Iya Lashe Kyautar Ballon D’or Ta Bana
Ya buga wa tawagar Ingila wasanni 106, ya ci ci kwallo 49, ya dade a matsayin mafi bajinta a kasar kafin daga baya Rooney ya karba, sai kuma Harry Kane da ke rike da gurbin.
Tun yana shekara 17 ya fara buga wa Manchester United wasa ya lashe kofin lig guda uku da European Cup da kuma FA Cup.
Yana daya daga cikin wadanda suka tsira da ransu a lokacin da ‘yan wasan Manchester United suka yi hatsarin jirgin sama a birnin Munich din kasar Jamus a shekara ta 1958.