Kungiyar malamai ta bukaci a dauki matakan ceto kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya cikin Jihar Kaduna.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata takarda da shugban kungiyar, Yusuf Muhammad da Sakatarenta James Garba suka sa wa hannu.
- Kudin Da NNPC Ke Kashewa A Tallafin Mai Ya Wuce Kima – Hamid Ali
- Malam Yaya Siffar Wankan Janaba Take?
Sanarwar ta yi bayani kan irin halin da kwalejin kimiyya da fasaha ta Zariya da aka fi sani da Nuhu Bamalli Polytechni ke ciki na matsaloli wadanda tuni suka fara damuwar al’ummar da suke cikinta.
Kungiyar ta ce abu mafi dacewa shi ne, a samu ceto kwalejin daga rugujewa a sakamakon rashin kayayyakin more rayuwa da suka yi karanci a cikin makarantar.
Kungiyar ta ce wani abin takaici shi ne, akwai lokutan da dalibai suke rubuta jarabawa a azuzuwan da suke zubar da ruwa, musamman lokacin damina.
Ta ce akwai bukatar samar da baban more rayuwa domin samun kyakkyawan yanayin ta yadda daliban makarantar da su sami ilimi maki inganci.