Don Allah malam ina so a siffanta min yadda ake yi wankan janaba, saboda ban jima da zama mutum ba (balagagge)?
To dan’uwa janaba wani hukunci ne da yake faruwa saboda daya daga cikin abubuwa guda biyu: ko dai mutum ya yi mafarki kuma ya ga maniyyi, ko kuma mutum ya sadu da matarsa, duka wadannan suna wajabta wanka Game da siffarsa kuwa, to wankan janaba yana da siffofi guda biyu, duk wacce ka dauka ta yi:
- Tashar Samaniya Ta Sin: ‘Yan Sama Jannati Na Kumbon Shenzhou-14 Sun Fara Tattaki A Wajen Tashar
- Wasu Fusatattun Matasa Sun Afka Wa Tawagar Sanata Kwankwaso A Jihar Kogi
1. Siffar da ta fi kamala ita ce wacce ta zo a hadisin A’isha cewa Manzon Allah (SAW) idan ya zo wankan janaba yana farawa ne da wanke hannunsa, sannan sai ya wanke farjinsa da hannun hagu, sai kuma ya yi alwala amma ban da wanke Kafa, sannan sai ya debi ruwa sau uku ya zuba a gashinsa, bayan haka sai ya zuba a ragowar jikinsa, sannan sai ya wanke Kafarsa. Bukari da muslim.
Akwai kuma siffa ta biyu wacce ta zo a hadisin Ummu-salama lokacin da Annabi (SAW) yake siffanta mata wankan janaba, inda yake ce mata : “Ya ishe ki ki zuba ruwa sau uku a kanki, sannan ki zuba a duka jikinki, mutuKar kin yi haka to kin tsarkaka” Muslim ne ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 330.
Allah ne mafi sani.