Wata babbar kotun tarayya da ke Legas a ta yanke wa wani mutum mai suna Oyeyemi Sharafadeen mai shekaru 55 hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari bisa samunsa da laifin safarar miyagun kwayoyi.
An gurfanar da Sharafadeen a gaban kuliya bisa tuhumar laifuka uku.
- Manyan Abubuwa Takwas Da Suka Girgiza Zaben Shugaban Kasa Na 2023
- ‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 12 Yayin Tashin Bam A Wurin Hoko Danyen Mai A Ribas
Karar mai alamar FHC/L/79c/23 tana tuhumarsa da laifin safarar miyagun kwayoyi.
Ya amsa laifinsa a gaban mai shari’a Chukwujekwu Aneke.
Bayan karar da ya shigar, kotun ta sake duba gaskiyar lamarin, inda mai gabatar da kara, Mista Augustine Nwagu, ya gabatar da hujjoji da dama don tabbatar da tuhumar da ake masa.
Kotun ta amince da shaidun da aka gabatar mata.
Nwagu ya bukaci kotun da ta yanke wa Sharafadeen hukunci bisa ga hujjoji da aka gabatar mata.
A hukuncin da ya yanke, alkali ya samu wanda ake tuhuma da laifi, kuma ya yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari kan kowanne daga cikin laifuka uku da ake tuhumarsa.
A cewar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da ta gurfanar da shi, Sharafadeen ya aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Janairu a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja.