Ba Nijeriya ha ce ke fuskantar matsalar tsaro ba, kasashe da dama na fuskantar irin tasu matsalar.
Amma yadda kasashen ke tunkarar lamarin yayin da matsalar ta addabe su shi ne abin dubawa. Daga dukkan alamu sauran kasshen duniya sun samar wa kansu hanyoyin magance matsalar tsaro, amma lamarin tabarbarewar tsaro ya zama tamkar a Nijeriya kadai ake fuskantar ta, don a halin yanzu lamarin ya fara zama jiki a kasarmu, kullum ka tashi zaka ji sabon labari, kuma har yanzu babu wani mataki na gaggawa da ake dauka don kawo karshen lamarin.
Al’umma sun gaji da yadda harkokin tsaro ke kara tabarbarewa, matsaloli irin su kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci sun zama ruwan dare, lamarin ma ya kara ta’azzara ne da karuwar wasu laifuffukan kamar su safarar muggan kwayoyi, sace sace ta intanet da kuma safarar sassan bil’adam.
Babbar matsalar tsaro a Nijeriya ita ce yadda jami’an tsaronmu ke amfani da tsofaffin hanyoyi wajen yaki da ‘yan ta’adda, ‘yan ta’addan da su ne ke amfani da kayan aiki na zamani wajen gallaza wa al’umma.
Masana sun bayyana cewa, rashin kayan aiki na zamani ne dalilin da yasa gwamnati da hukumominta suka kasa yin komai, abin duk ya fi karfinsu, basa iya yin takabus wajen kare al’ummar jihohi irinsu Borno, Zamfara, Katsina, Kaduna, Neja da Nasarawa da kuma yankunan Kudu maso Gabas.
Babu tantama wasu jihohi a kasar nan na fuskantar mamaya daga ‘yan ta’adda akwai kuma bukatar kai masu daukin gaggawa don tabbatar da ceto rayuwar al’ummar yankunan. Wasu daga cikin manyan dalilan da aka gano suna kara wutar ayyukan ta’addanci a kasar nan sun hada da rashin aikin yi a tsakanin matasa da tsananin talauci a tsakanin al’umma. Wadanan sune suka fi bukatar a gaggauta kai masu dauki, yakamata a basu daukin daya wuce yadda ake basu a halin yanzu.
A ra’ayimu a kwai bukatar samar da ayyukan yi ga matasa da kuma samar da yanayin da harkokin kasuwanci za su bunkasa ba tare da wani cikas ba, bai kamata a ce, kasa kamar Nijeriya da ke tattare da dinbin albarkatun kasa da yawan al’umma amma kuma ta kasance hedikwatar talauci ta duniya ba.
Harin ‘yan ta’adda a Ondo tare da kashe mutum 58.
A ra’ayin wannan jaridar, cin hanci da rashawa na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da matsalar tsaro a fadin tarayyar kasar nan. Masu rike da mafun iko suna cigaba da babakere tare da azurta kansu ta hanyar amfani da kudaden gwamnati, sun yi watsi da kula da hakkokin al’umma wanda shi ne aikin da suka rantse za su kare. Ayyuka kuma sun yi wa jami’an tsaromu yawa kuma gashi ba a basu albashin da yakamata a kan haka basu sa kishin kasa a gudanar da aikisu, a kan haka matsalar ke cigaba da barazanar hadiye al’umma gaba daya.
Daya daga cikin manyan tambayoyin da ke bukatar amsa anan shi ne, ta yaya bamabamai da manyan bidigogi na zamani suka shigo kasar nan suka kuma fada hannun ‘yan ta’adda?, a halin yanu dai an dora wannan laifin a kan yadda iyakokin kasar suke tamkar a bude babu cikakken tsaro, wanda hakan yake sa bakin haure suke samun saukin shigowa daga kasashe makota kamar su Nijar, Jamhoriyar Benin da Chadi sau da yawa kuma dasu ake amfani wajen aikata muggan laifukka a sasan kasar nan.
Rashin samar da cigaba a sassan yankuna kasar nan shi ma ya taimaka wajen haifar da matsalar tsaron da muke fuskanta, musamman ganin yadda wasu kabilu da al’ummu ke korafin ana barinsu a baya wajen samar da ababen more rayuwa. Irin wannan ke haifar da rashin jin dadi a tsakanin mutane, abin da kuma yake kai ga tayar da hankula da aikata ayyukan ta’addanci da kuma nuna halin ko-in-kula, wanda ta hakan suke fatan gwamnati za ta kula dasu ta san da zaman su.
Tabbas kare rayuwa da dukiyar al’umma shi ne muhimmin aikin gwamnati, ya kuma kamta gwamnati ta dauke shi da matukar muhimmanci, tunda wannan aiki yana nan a cikin kudin tsarin mulkin kasar nan a sashi na 14 (2) (b) na dokokin 1999 Nijeriya (kamar yadda aka gyara), na tabbatar da tsaro da hakkokin raywaur al’umma to ya zama dole gwamnati ta dauki lamarin da matukar muhimmanci, bai kamata jami’an gwamnati su kauce daga wanan hakkin da ke kansu ba, musamman ganin a halin yanzu ana neman daukar ayyukan ta’addanci tamkar wata harkar kasuwanci, maimako a fuskanci yaki da ‘yan ta’addan sai aka bige da jefa wa juna laifukka.
Abin akwai takaici ta yadda mahukunta suka kasa kai hari tare da kama masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci a kasar nan, yakamata ace an kama su an kuma gurfanar dasu a gaban shari’a don su dandana sakamakon ayyukansu.
A ra’ayinmu, wannan halin da ake ci, ya cancanci a sake duba bukatar samar da ‘yansanda yankuna, muna kara kira ga gwamnati da ta duba wannan bukata. Samar da ‘yansandan yankuna zai taimaka wajen kawo karshen matsalar tsaron da ake fuskanta a fadin tarayyar kasar nan. Ya kuma kamata a samar da kudade don sayen kayan aiki na zamani ga jami’an tsaron, a kuma samar da hanyoyin gano shirin aikata ta’addanci tun kafin a aiwatar dashi, ta yadda za a iya dakike aikatawa.
Muna kuma kira ga a kan bukatar samar da yanayin tafiya da kowa da kowa a yaki da ta’addanci, dole gwamnati, jami’an tsaro, kungiyoyi masu zaman kansu, Malaman addini, sarakunan gargajiya su daukar wa kansu aiki yaki da ta’addanci. Muna da bukatar hadin kan kowa da kowa a wajen kawo karshen wannan matsalar kafin ta hadiye mu gaba daya.