Rundunar ‘yansandan jihar Neja ta samu nasarar kama wani mutum mai suna Clement Joseph da ke garin Koropka, karamar hukumar Chanchaga, wanda yake bayyana kansa a matsayin likita.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar DSP Wasiu Abiodun, ya sanar da manema labarai a garin Minna.
- Xi Jinping Ya Ci Gaba Da Halartar Taron Karba-karba Na Shugabannin Mambobin Kungiyar APEC Karo Na 29
- Adabin Zamanin Da Na Sin (3) Wakokin Daular Tang
Ya ce, sun kama likitan bogin kan wasu laifuka guda uku da ake zarginsa da aikata wa.
Ya ce, “An kama wanda ake zargin da laifin yin karyar cewa, shi likita ne ya kuma karbi kudi a hannun wani mutum da sunan zai yi masa magani”.
Abiodun ya ce, kokacin da ake yi masa tambayoyi, ya tabbatar da cewa, shi ba likita ba ne.
A karshe dai, za a ci gaba da bincike domin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru, wanda kuma idan laifin da ake zarginsa da shi ya tabbata zai gurfana gaban kitu, domin yi masa gukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp