Rahotanni daga kungiyar bunkasa sana’ar kera motoci ta kasar Sin sun ruwaito cewa, zuwa safiyar yau Alhamis 14 ga wata, adadin motoci masu aiki da sabon makamashi da kasar take kerawa a duk shekara, ya zarce miliyan 10, al’amarin da ya zama karo na farko a tarihin kasar.
Wannan ya sa kasar Sin ta zama kasa ta farko a duk fadin duniya, wadda yawan motoci masu aiki da sabon makamashi da take kerawa a duk shekara ya wuce miliyan 10. Kana, kwararru suna sa ran ganin wannan adadin zai zarce miliyan 12 nan da karshen shekarar da muke ciki.
Sakamakon jagorancin manyan tsare-tsaren gwamnatin kasar Sin na tsawon shekaru 10, an bullo da manufofi masu karfafa gwiwa kusan 100, da kara sabunta fasahohin kera hajoji, tare da ci gaba da inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, al’amuran da suka taimaka gaya ga ci gaban sha’anin kera motoci masu aiki da sabon makamashi a kasar ta Sin. A nan gaba kuma, ba kara samar da irin wadannan motoci kawai kasar Sin za ta yi ba, har ma za ta ci gaba da kyautata ingancin motocin, a wani kokari na bayar da karin gudummawa ga sana’ar raya sabon makamashi a duk duniya. (Murtala Zhang)