• English
  • Business News
Saturday, August 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Karon Farko Gwamnatin Kano Za Ta Nada Matashi Mai Karancin Shekaru Mukamin Kwamishina

Dokta Yusuf Jibril Na Da Shekara 33 A Duniya

by Sadiq
3 years ago
in Labarai
0
A Karon Farko Gwamnatin Kano Za Ta Nada Matashi Mai Karancin Shekaru Mukamin Kwamishina
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya tura sunan Dakta Yusuf Jibril JY a matsayin daya daga cikin wadanda za a yi wa mukamin Kwamishina a Jihar.

Jibril, ya kasance matashi mafi karancin shekaru daga cikin jerin sunayen wadanda za a nada mukamin sabbin Kwamishinonin jihar.

  • ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 20 Kan Zargin Garkuwa Da Mutane A Jihohin Benuwai Da Gombe
  • An Saki Karin Ruwa Cikin Kogin Yangtze Sakamakon Fari Dake Addabar Wasu Sassan Kogin

Matashin zai kasance irinsa na farko a Najeriya da za a yi wa mukamin Kwamishina, inda yake da shekara 33 a duniya.

Tuni Majalisar Dokokin Jihar, ta tantance Jibril tare sa wasu mutum tara, wadanda za a yi wa mukamin Kwamishinoni.

Wannan na zuwa ne bayan ajiye aiki da Kwamishinonin jihar suka yi gabanin shiga zaben fidda-gwani, don neman guraben yin takara a zaben 2023.

Labarai Masu Nasaba

Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa

Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

Jibril dan asalin garin Rurum ne da ke Karamar Hukumar Rano a Jihar Kano.

Jibril, ya yi karatu har zuwa matakin Digiri, wanda daga nan ne ya shiga harkar kasuwanci, inda ya ke kasuwancin dakon mai a karkashin kamfaninsa mai suna JY Global Services.

Nadin nasa a matsayinsa na matashi zai bude kofa ga matasa musamman wadanda ke rajin ganin an yi tafiya da su a gwamnatance don sharbar romon dimokuradiyya.

Tuni matasa a jihar suka shiga yaba wa Ganduje kan mika sunansa ga majalisar dokokin jihar don tantance shi, inda suke ganin an sanya kwarya a burminta.

Kungiyoyi masu zaman kansu a baya-bayan nan sun sha kiran gwamnatin Jihar da ta yi kokarin jan matasa a jiki don damawa da su.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Dakta Yusuf JibrilGandujeGwamnatin KanokanoMajalisar Dokokin KanoMatashiMukamin Kwamishina
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ya Kamata Birtaniya Ta Girmama Alkawarin Da Ta Dauka Game Da Batun Tsibiran Malvinas

Next Post

Kyan Alkawari Cikawa

Related

Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa
Labarai

Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa

4 hours ago
Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya
Rahotonni

Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

4 hours ago
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP
Labarai

Babu Dalilin Da Zai Sa ‘Yan Nijeriya Su Yi Talauci – Tinubu

5 hours ago
Akwai Bukatar Samar Da Sauyin Zaman Lafiya Mai Dorewa A Duniya — Maryam Bukar
Labarai

Akwai Bukatar Samar Da Sauyin Zaman Lafiya Mai Dorewa A Duniya — Maryam Bukar

8 hours ago
UBEC Ta Kaddamar Da Makarantun Zamani 21 A Sassan Nijeriya
Labarai

UBEC Ta Kaddamar Da Makarantun Zamani 21 A Sassan Nijeriya

8 hours ago
Gwamnatin Katsina Za Ta Samu Kudaden Bunkasa Ilimi
Labarai

Tetfund Ta Samar Da Naira Biliyan 100 Don Inganta Ilimin Likitanci – Masari

9 hours ago
Next Post
Kyan Alkawari Cikawa

Kyan Alkawari Cikawa

LABARAI MASU NASABA

Wang Yi: Ya Kamata A Mutunta Tarihi Domin Magance Sake Yin Kuskure

Wang Yi: Ya Kamata A Mutunta Tarihi Domin Magance Sake Yin Kuskure

August 15, 2025
An Samu Rarrabuwar Kawuna A Jam’iyyar ADC Kan Shugabancin David Mark

An Samu Rarrabuwar Kawuna A Jam’iyyar ADC Kan Shugabancin David Mark

August 15, 2025
Ya Kamata A Yi Wa Japan Jinyar Cutar “Mantuwar Tarihi”

Ya Kamata A Yi Wa Japan Jinyar Cutar “Mantuwar Tarihi”

August 15, 2025
Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa

Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa

August 15, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Bikin Mu’amalar Al’adu Da Jama’a A Hedkwatar MDD

CMG Ya Kaddamar Da Bikin Mu’amalar Al’adu Da Jama’a A Hedkwatar MDD

August 15, 2025
Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa

Gwamna Sani Ya Ba Da Umarnin Gudanar Da Bincike Kan Kashe Wani Matashi A Barnawa

August 15, 2025
Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

Rawar Da Dakta Bello Matawalle Ke Takawa Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Nijeriya

August 15, 2025
Gasar Wasannin Mutum Mutumin Inji Ta Duniya Ta 2025 Na Gabatar Da Sabbin Fasahohin Zamani

Gasar Wasannin Mutum Mutumin Inji Ta Duniya Ta 2025 Na Gabatar Da Sabbin Fasahohin Zamani

August 15, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Babu Dalilin Da Zai Sa ‘Yan Nijeriya Su Yi Talauci – Tinubu

August 15, 2025
Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata A Watan Yuli

Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata A Watan Yuli

August 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.