Mataimakin minista mai kula da aikin gona da kauyuka Zhang Xingwang ya bayyana a gun taron manema labarai da ofishin yada labarai na kasar Sin ya yi a yau Juma’a na cewa, yanzu an kammala aikin girbi shinkafa shukin farko na lokacin zafi. Ya zuwa ran 24 ga watan nan, yawan hatsin da aka girba a lokacin kaka ya kai kashi 82.5%, abin da ya bayyana armashin girbin da aka yi a bana. Yawan hatsin da Sin ta girba ya kai fiye da ton miliyan 650 a cikin shekaru 9 a jere, an yi kiyasin cewa, a bana kuwa wannan shi ne karon farko da adadin zai kai ton miliyan 700.
An ce, bana an yi girbi mai armashi. An riga an kammala aikin girbin shimkafa shukin farko, yawan hatsi na lokacin zafi ya kai ton miliyan 149.7, adadin ya karu da kg biliyan 3.6, shinkafar shukin farko da aka girba ya kai kg biliyan 28.2, shekaru 4 a jere ke nan da adadin ya kai kg biliyan 28. Hatsin lokacin kaka kuwa, ana samun bunkasuwa yadda ya kamata, yawansa ya karu sosai. (Amina Xu)