A ranar 9 ga wata bisa agogon wurin, an shirya gagarumin bikin cika shekaru 80 da cimma nasara a yakin kare kasa na tsohuwar Tarayyar Soviet a filin “Red Square” na birnin Moscow. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da ma shugabanni daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 20 sun halarci bikin bisa gayyatar da aka yi musu.
Ga duniya, shekarar 2025 tana da ma’ana ta musamman. Shekara ce ta cika shekaru 80 da nasarar da jama’ar kasar Sin ta cimma na yakar maharan Japan, da ta babban yakin kare kasa na tsohuwar Tarayyar Soviet, da ta yakin kin harin ‘yan mulkin danniya na duniya, har ma da cika shekaru 80 da kafuwar Majalisar Dinkin Duniya.
- INEC Na Samun Matsin Lamba Don Kar Ta Yi Wa TNN Rajista — Kakakinta
- Nijeriya Za Ta Karɓi Baƙuncin Taro Karo Na 4 Na Ƙananan Sana’oi Na Ƙungiyar AU
Sinawa kan ce, “A Koyi darasi daga tarihi”. Darussan zafi na yakin duniya na biyu sun gargadi mutane cewa, son zuciya da wariya, kiyayya da yaki za su kawo masifa da wahala ne kawai, yayin da mutunta juna, zaman tare cikin daidaito, ci gaba cikin lumana, da samun wadata tare su ne hanya madaidaiciya a duniya. Amma abin takaici ne cewa, a yau, bayan shekaru 80 da suka gabata, wasu mutane sun manta da darussan, kuma suna bin ra’ayin kashin kai, danniya ko babakere da zalunci, kana da sun ta yayata kalaman na wai “rashin amfanin Majalisar Dinkin Duniya” da “rashin inganci na dokokin kasa da kasa”.
A wannan muhimmin lokaci, shugaba Xi Jinping ya kai ziyarar aiki kasar Rasha, inda ya halarci bikin cika shekaru 80 da cimma nasara a yakin kare kasa na tsohuwar Tarayyar Soviet, lamarin da ya sanar da duniya cewa, ba za a manta da tarihi ba, kuma zaman lafiya ba a samunsa cikin sauki. Don haka, dole ne Sin da Rasha su kiyaye adalci na kasa da kasa tare.
A yayin tattaunawar da suka yi a birnin Moscow a wannan karo, shugabannin kasashen biyu sun amince da yada ra’ayin gaskiya game da tarihin yakin duniya na biyu, da kiyaye fada-a-ji da matsayin Majalisar Dinkin Duniya, da kiyaye adalci a duniya. Wannan ya nuna alkibla ga al’ummomin duniya, ta kare nasarorin da aka samu a yakin duniya na biyu, da kuma tinkarar hadari da kalubale masu yawa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp