Matashiyar ‘yar kasuwa mai fatan ganin ta dogara da kanta Fatima Sa’ad, ta yi wa Leadrship Hausa bayanin rayuwarta da yadda ta tsunduma a harkar kasuwanci, ci gaban ta samu da ma kalubalen da fuskata a harkar, in a cikin hakan ta ba wa iyaye shawarar su tashi tsaye wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yansu. Ga dai yadda hirar tasu ta kasance da wakiliyarmu Amina Bello Hamza.
Da farko za mu so ki bayyana mana sunanki
Sunana Fatima Sa’ad Aliyu. An haife ni a Tudun Jukun da ke Zariya, na yi karatuna tun daga Nursery har na kammala sikandirena, yanzu haka ina karatu a Nuhu Bamalli polytechnic Zariya.
Ko Malamar Na Da Aure?
A a ba ni da aure
Wace sana’a kike yi a halin yanzu?
Ina sayar da duk wani nau’i na sutura, (Hajibai, Atamfa, shadda, Leshi, yadi na maza da mata, jakunkuna, takalma, da dai sauran su. Sanan ina sana’ar hannu Hada jakunkuna, takalma, zannuwan gado, da fululunka kujeru da kuma sa’ar Aya da Riidi).
Menene ya baki sha’awar fara wannan sana’a?
To ni dai ba zance ga wani abu da ya ba ni sha’awa ba saboda tun ina firamare na nake sana’a irin ta dalibai a makarata irin su iloka, Aya, lokacin ban san ma mai zan yi da kudin ba kawai ni dai ina jin dadi in ji ana cewa ki bani abu kaza.
To daga baya ne da girma ya fara zuwa sanan na ji sha’awar ka san cewa kamar mamana saboda ita ‘yar kasuwa ce ba ta iya zama ba sana’a gaskiya.
Idan mutum na son fara wannan sana’ar wani abu zai tana da don samun cikakkiyar nasara?
To da farko de dole ne ya fara sa rai shi sa’ana zai yi kuma ya dauke ta da mahimmaci, saboda idan bai dauke ta da mahimmanci ba ba zai iya juriya akan ta ba, sanan sai jari ko da bashi da yawa in dai bai raina ba to lallai wata rana zai ga amfanin haka, cikakkiyar nasara ba’a samun ta haka dole sai ka hadu da jarabawa da kuma kalubale, to a nan za ka yi hakuri da juriya sai Allah ya taimake ka har ka kai ga cin nasara a rayuwarka.
Ta Yaya Kike Tallata Hajojinki?
Ina tallata hajata ne ta kafar sada zumunta (social media). Sannan duk inda zan shiga makaranta ce gidan biki kai koma ina ne to zan tallata hajata, haka ma cikin kawayena.
Kuma Alhamdu lillahi muna ganin alfanun haka.
Ko kin taba samun tallafin gwamnati ko wata hukuma a harkar kasuwanci?
Gaskiya ban tabba samun ko daya daga cikin wani abu na tallafi ba.
Ko za ki bayyana mana wani abin da ya taba faruwa dake na farin ciki ko akasin haka a rayuwarki na wannan sana’ar?
Alhamdu lillah, ita dama sana’a ta gaji haka wata rana ka yi farin cikin wata ranan ka yi akasin haka. Na farin cikin shi ne yadda ina zaune a kira ni a ce ana son abu kuma wannan abu ban yi tunani za’a ce za’a saya a gurina ba amma sai a saya a guri lallai ina farin cikin sosai. Akasan haka kuwa shi ne a kira ka a ce ana son kaya sai an saya ko dai kun gama magana sai a ce an fasa. Ko kuma kaya da ka saya ya zo gurin sai an kawo ka ga bashi bane kai kuma ka riga ka gama magana da mai saya kuma su ce ba shi suke so ba, hakan yana bata min rai saboda mutane sun yadda da kai suke sayayya a gurinka, to bana ji dadi gaskiya.
Ya kike ganin yanayin tarbiya a wannan lokacin?
Gaskiyar magana tarbiya ta yi karanci a wanan lokaci. Muna wani zamani ne da sai dai mu ce Lahaula Walakuwati illa billah, sai dai mu ci gaba da addu’ar samun sauki wurin Allah. An yi sakace da tarbiyya koyarwar Manzon Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma magabatanmu. To iyayenmu su kara lura da yara a ko ina suke, sannan su dinga yi musu addu’a saboda addu’ar iyaye tana da tasiri a gurin ‘ya’yansu.