ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Matsayinta Na Kasa Mafi Yawan Masu Harbuwa Da Cutar COVID-19 A Duniya, Matakin Amurka, Tamkar “Barawo ke cewa ku tare barawo!”

by CMG Hausa
3 years ago
COVID-19

Tun daga ranar 5 ga watan nan na Janairu, Amurka ta sanyawa masu yawan shakatawa daga Sin takunkumin shiga kasar, saboda barkewar cutar a cikin gidan Sin, bisa zargin cewa wai “Shigar da Sinawa Amurka na iya haifar da bullar sabbin nau’o’in cutar, wanda ka iya haifar da hadarin yaduwar cutar.” 

To sai dai kuma bisa shaidun kimiyya kan kwayoyin cutar, kwayar cutar mafi yawa a cikin Sin ita ce nau’in BA.5, wadda babbar kwayar cuta ce da aka samu a Amurka a watannin baya bayan nan, yayin da kwayar cutar XBB.1.5 da aka samu a yankin Shanghai da Hangzhou, ta kasance babbar kwayar cuta mafi yaduwa a Amurka. Don haka dai, ana iya gane cewa, kasar Sin na fama da annobar cutar a duniya, yayin da Amurka ta yi watsi da gaskiyar lamarin, ta kuma saba wa kimiyya, bisa wani shirin siyasa na “Barawo ke cewa ku tare barawo”.

  • Sin Na Adawa Da Siyasantar Da Matakanta Na Yaki Da Covid-19 

Bisa kididdigar cibiyar lura da cutar mura ta Duniya, an gano cewa, nau’in XBB.1.5 na COVID-19 ya yadu a kasashe da yankuna a kalla 74, ciki har da jihohi 43 na Amurka. Yawancin masana Amurkawa sun nuna cewa, samfurin farko da aka gano na XBB.1.5, an same shi a biranen New York, da Connecticut a karshen watan Oktoba na bara.

ADVERTISEMENT

Lokacin da aka gano XBB.1.5 a Amurka, kasar Sin tana dinga aiwatar da tsauraran matakan rigakafin kamuwa da cutar. Ko dai nau’in cutar na BA.5 ce a halin yanzu ta zama ruwan dare a Sin, ko kuma sabon nau’in XBB.1.5 ne aka gano, an dai samu kwayar cuta ne bayan Amurka, da sauran kasashen duniya.

A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin na kokarin daidaita manufofin rigakafi, da shawo kan annobar, tare da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Annobar tana kara lafawa, kuma tattalin arzikin kasar yana farfadowa.

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Tun daga ranar 8 ga watan nan na Janairu, kasar Sin za ta daina daukar matakan rigakafin cututtuka masu yaduwa ga wadanda za su shigo kasar Sin daga ketare, da kayayyakin da za a shigar da su kasar Sin, galibin kasashen duniya sun gamsu da wannan matakin da kasar Sin za ta dauka.

Sabanin haka, Amurka a ko da yaushe tana siyasantar da rigakafin cutar tare da mayar da matakan abun zargi. Baya ga mayar da ita matsayin “kasa ce wadda take matsayin farko a duk duniya ta gaza yaki da cutar”, sakamakon haka, ita ce ta haddasa yaduwar cutar a fadin duniya, har ma ta hana sauran sassan duniya ci gaban yaki da annobar. (Safiyah Ma)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara
Daga Birnin Sin

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Mara Wa Dan Siyasa Baya Zubar Da Mutunci Ne – Martanin Kwankwaso Ga Obasanjo

Mara Wa Dan Siyasa Baya Zubar Da Mutunci Ne - Martanin Kwankwaso Ga Obasanjo

LABARAI MASU NASABA

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.