Hakuri: Yana da matukar riba a rayuwa, ba ma a zamantakewar aure kadai ba, abin da yake damun wasu ma’auratan shi ne gaggawa da rashin hakuri, za ka ga mutum yana fadin cewa yana cikin matsala amma kuma abin mamaki shi ne ba zai iya hakuri akan matsalar ba. Musamman a bangaren mata, ki sani cewa wani abin fa dole take kamawa idan kika kasa hakuri na dan wanin lokaci wallahi hakan sai ya jawo miki shiga matsalar da sai kin dauki tsawon lokaci ba ki fita daga ciki ba.
‘Yar uwa ki yi tunani ki gani lokacin da za’a kawo ki gidanki kowa idan ya gama yi miki huduba abin da yake cike hudubar da shi shi ne a rika hakuri, kada ki yi zaton don su ba su samu soyayyar mijinsu bane (su wadanda suke miki nasihar) a’a wallahi wata a cikinsu soyayyar da mijinta ke gwada mata ke ko rabinta ba za ki samu ba, amma da za ki tambaye ta meye jagoran wannan zaman nasu sai ta ce miki hakuri, haka shima ta bangaren mijin.
- Zulum Ya Yi Alƙawarin Gyara Sansanin NYSC Na Borno
- Sin Ta Yi Watsi Da Tsegumin Da Marco Rubio Ya Yi Kan Hadin Gwiwarta Da Latin Amurka
Gidan Mijinki wuri ne wanda kike bakuwa a cikinsa, kin bar inda aka sanki aka san matsalarki, kin je inda ba’a san ko daya daga ciki ba, a da nauyinki ake dauka amma a yanzu dole ke kike daukar nauyin wasu, (wanann shi ne girman) hakuri da kawaici kuma su za su jagorance ki matukar kina son samun sauki a cikin al’amuranki.
Kada Zakin Soyayya Ya Kwasheki: har ki yi zaton kin tsira daga barazana ko fadan mijinki a’a wallahi sai kin yi hattara ke za ki fi kowa shan fadansa (domin kin fi kowa kusanci da shi) (a halin da kuka kasance a karkashin inuwar aure) matukar ba za ki rinka kiyaye abin da baya so ba.
Wata ‘yar uwa ana auranta aka kira ta ana yi mata nasiha sai ta ce ni dai kun dame ni da na yi hakuri na yi hakuri, tun da yana sona ina son shi kam ai shike nan, wallahi ko shekara daya ba’a yi ba ran nan na kai mata ziyara sai take cewa Amina ashe da ake cewa na yi hakuri nake ganin an dame ni da gaskiyarsu yanzu wallahi har gani nake hakurin da aka ce na yi ma ya yi kadan.
To rayuwar aure sai da hakuri, idan muka yi hakurin nan da ake fada in sha Allahu za mu ga nasararsa a gaba, amma idan ba mu yi hakurin nan da ake fada mana ba za mu kasance cikin da na sani da damuwa a rayuwarmu. Saboda wasu da zarar auran fari za kufce musu sai ku ga ba za su taba samun nutsuwa ba, ko ga namiji ko macen wanda bai yi hakuri ba a cikin su. Wasu sai ku ga har karshe rayuwarsu ana nadama da da na sani.