Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin ta ce a shirye kasar take ta hada hannu da Amurka, domin kyautata huldar cinikayya da tattalin arziki mai aminci da dorewa a tsakaninsu, bisa ka’idojin girmama juna da zaman lumana da kuma moriyar juna.
Kakakin ma’aikatar He Yadong, ya bayyana yayin taron manema labarai na yau Alhamis cewa, matakan sanya haraji ba su dace da muradun kasashen biyu ko na sauran sassan duniya ba.
- Xi Jinping Ya Yi Rangadi A Arewa Maso Gabashin Kasar Sin Gabanin Bikin Bazara
- UNICEF Ta Nemi Dala Miliyan 250 Don Tallafa Wa Yara A Sakkwato, Zamfara Da Katsina
He Yadong ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambaya game da yuwuwar samun karin kaso 10 na haraji kan kayayyakin Sin dake shiga Amurka da gwamnatin Trump ta sanya wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Fabrairu.
Rahotanni na cewa, a shekarar 2024, jimilar kayayyakin da Sin ta fitar ya kai yuan triliyan 18, karuwar kaso 2.3 a kowacce shekara. Yawan kayayyaki ya kai matsayin koli, kuma ana sa ran kasar zata ci gaba da rike kambunta a matsayin kasa ta biyu a duniya mafi fitar da kayayyaki zuwa ketare cikin shekaru 16 a jere.
A cewar He Yadong, fadada fitar da kayayyaki da Sin ke yi, wani yunkuri ne na kasar a matsayinta na babbar kasa, kuma muhimmiyar gudunmuwa ce ga ci gaban tattalin arzikin duniya.
Ya ce kasar za ta fadada bude kofofin kasuwaninta na kayayyaki bisa tsari, da aiwatar da shirin soke harajin kaso 100 bisa 100 ga kayayyaki daga kasashe mafiya karancin ci gaba da suka kulla huldar diflomasiyya da ita. Bugu da kari, za ta gina babbar kasuwa cikin kasuwar duniya ta bai daya da bayar da sabon karfi ga ci gaban tattalin arzikin duniya. (Fa’iza Mustapha)