Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi na yau cewa, rage talauci ya kasance muhimmin bangare na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. Kuma a cikin shekarun da suka gabata, bisa tsarin dandanlin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, bangarorin biyu sun yi mu’amala da hadin gwiwa kan ayyukan rage talauci, tare da samun sakamako mai armashi.
Lin Jian ya bayyana hakan ne yayin da yake ba da amsa ga tambayar da wani dan jarida ya yi masa game da hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a fannin rage talauci. Lin ya ce, kasar Sin ta bullo da kuma aiwatar da ayyukan rage talauci da aikin gona har 47, ta kuma horar da kwararru a fannin aikin gona kusan 9000, da inganta fasahohin zamani sama da 300 da ake amfani da su.
- NYSC Ta Mayar Da Sansaninta Na Bauchi Zuwa Kwalejin Kangere
- DSS Ta Kama Tsohon Editan BBC, Adejuwon Soyinka A Filin Jirgin Sama Na Legas
Yayin da fasahar Juncao ta kasar Sin ta bude kofar samun kudin shiga ga dubban daruruwan jama’ar nahiyar. Haka ma, irin shuka na shinkafa na musamman na kasar Sin ya kara yawan shinkafa da ake nomawa a kasashen Afirka da dama daga matsakaicin tan 2 a kowace kadada zuwa tan 7.5.
Lin Jian ya kara da cewa, kasar Sin ta kasance jigo mai karfi ga nahiyar Afirka wajen lalubo sabuwar hanyar zamanantarwa da samun bunkasuwa, kuma mai ba da muhimmiyar gudummawa wajen samar da sabbin hanyoyin rage talauci. A cewar sa, a shirye take Sin ta dauki taron kolin dandalin tattanawar hadin gwiwar Sin da Afirka da za a yi a wannan shekarar ta 2024 a matsayin wata dama ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da Afirka don sa kaimi ga inganta shirin rage talauci da samar da makoma mai kyau ga jama’ar Afirka. (Yahaya)