A wani al’amari mai cike da takaici da kusan kowa ya sani, makircin siyasa a Jihar Kano ya sake jefa babbar masarautar jihar cikin wani yanayi wanda ba ita kaɗai abin ya taɓa ba har da ma yankin Arewa.
Maido da Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano da Gwamna Abba Yusuf ya yi, tare da sauke wasu sarakuna biyar da gwamnatin da ta gabata ta naɗa, ya zama abin da al’umma ke ta tofa albarkacin bakinsu a kai game da halin da sarakunan gargajiya suka tsinci kansu a ciki yayin da suka shiga tsaka mai wuya a tsakiyar ɓangarancin siyasa.
- Sarki Sanusi Ya Naɗa Dagacin Janguza Duk Da Rikicin Masarautar Kano
- Yajin Aiki Ya Hana Sauraren Shari’ar Sarakunan Kano
Wannan labari mara daɗi ba lamari ne da ya sha bamban ba; alama ce ta wani yanayi mai tayar da hankali da ya addabi jihohi dabandaban a faɗin ƙasar nan.
Idan za mu iya tunawa, tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya tsige wani basaraken gargajiya mai daraja ta ɗaya, Ohimege Igu, na koton-Nkarfe, Alhaji Abdulrazaq Isa Koto.
Za mu kuma tuna cewa a shekarar 2022, sa’o’i 24 bayan hawansa mulki a matsayin Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya sauke wasu sarakunan gargajiya uku da magajinsa, Adegboyega Oyetola ya naɗa.
Tun daga Kogi zuwa Osun, da kuma Kano, mun ga yadda sarakunan gargajiya ke rungume hannu suna kallo ana korar su bisa son zuciya na gwamnatocin da ke hawa karagar mulki, galibi a matsayin ramuwar gayya kan abin da suka yi na mubaya’a, ko kuma a matsayin hanyar da za a tabbatar da ƙara karfin mulki.
A ra’ayin wannan jaridar, wannan wasan siyasa mai ban mamaki da ake yi wa masarautun gargajiya ba wai kawai yana zubar da ƙimarsu ba ne har ma yana lalata tushen l’adun ƙasar nan da aka gada kaka da kakanni ne.
Ana son masarautun gargajiya su masu kula da ɗimbin tarihi da al’adun Nijeriya, waɗanda ke tattare da gyara ɗabi’u da al’adu da hikimomi waɗanda ake gadar wa ƴan baya.
Waɗannan masarautun sun kasance ababen girmamawa ne ba kawai a cikin al’ummominsu ba har ma a duk faɗin ƙasar nan.To sai dai idan suka zama ƴan amshin shata a wasannin siyasa na masu riƙe da madafun iko, to kwarjininsu da ikonsu yana matuƙar raguwa, kuma amanar da talakawan suka ba su tana shiga cikin haɗari.
Dole ne mu kula tare da killace masarautunmu na gargajiya daga rugujewa a sakamakon siyasar ɓangaranci. Dole ne a yi tir da kakkausar murya kan yadda wamnoni ke korar sarakunan gargajiya tare da mayar da su kan karaga bisa manufarsu ta siyasa.
Irin waɗannan abubuwa ba wai kawai suna zubar da mutuncin waɗannan masarautun ba ne, har ma suna haifar da saɓani da rashin zaman lafiya a tsakanin al’ummomin da suka daɗe suna dogaro da hikima da jagoranci na sarakunansu na gargajiya.
Duk da yake gaskiya ya kamata sarakunan gargajiya su nesanta kansu daga siyasar ɓangaranci, kuma su ci gaba da kasancewa iyayen ƙasa, kowa nasu ne, ya kamata aikinsu na masu kula da abubuwan da aka gada na gargajiya da samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummominsu ya kasance mara zargi.
Kamata ya yi a bar su, su sauke nauyin da ke kansu ba tare da tsoron fushi ko tsangwama ba daga ƴan siyasa ba.Ya kamata a lura da cewa, akwai ƙwararan dalilai na tsige sarakunan gargajiya, kamar samunsu da hannu wajen aikata laifuka, rashin biyayya, ko munanan ɗabi’u da ke barazana ga rayuwar al’ummarsu.
A irin waɗannan lokuta, dole ne a bi tsarin da ya dace, kuma matakin da za a ɗauka ya kamata ya dogara ne a kan ƙwararan hujjoji kuma a gudanar da shi ta hanyar tsarin doka, ba son rai na siyasa ba.
Al’amuran da suka faru a Sakkwato, inda gwamnan jihar ya sige hakimai 15 kan karagar mulki bisa zargin rashin biyayya, satar filaye, da taimakon rashin tsaro da kuma dakatar da wani basaraken gargajiya a Jihar Oyo bisa zargin alaƙa da masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, misali ne na matakan da suka dace da aka ɗauka domin tabbatar da kare mutuncin masarautun gargajiya da kare da muradun mutanen da suke yi wa hidima.
To sai dai kuma halin da ake ciki a Kano, inda ake ganin mayar da sarki ɗaya da tsige wasu daga muƙaminsa na siyasa ne kawai, ya sha bamban da abubuwan da ake ganin na ƙa’ida ne.
Irin haka kuma yana lalata kimar waɗannan cibiyoyi kuma yana haifar da ƙarin rarrabuwar kawuna da ɓacin rai a tsakanin al’ummomin da tuni suke kokawa da ƙalubalen rashin tsaro da tashe-tashen hankula na zamantakewar al’umma.
Lokaci ya yi da al’umma za su fahimci gagarumar gudunmawar da masarautun gargajiya za su iya bayarwa wajen samar da haɗin kai, da kiyaye al’adunmu, da magance matsalolin da suka addabi ƙasar nan.
Waɗannan cibiyoyi, idan aka mutunta su da kuma ba su ƙarfi, za su iya zama ƙawance mai ƙarfi a yaƙi da rashin tsaro, waɗanda za su zama ginshiƙan tattaunawanda warware rikice-rikice, da faɗaɗa ci gaban al’umma.
Domin samun nasarar wannan, dole ne mu sanya ƙarin kariya ga masarautunmu a cikin kundin tsarin mulkin ƙasa.
Dole ne a samar da sahihan tsaretsare na naɗawa da tsara wa’adin mulki, da tsige sarakunan gargajiya, tare da kawar da kai daga son zuciyar ƴan siyasa da tabbatar da cewa aikinsu ya kasance bisa maslahar al’ummarsu ba tsarin ɓangaranci ba.
Bugu da ƙuari, dole ne mu ƙarfafam asarautun gargajiya su rungumi aikin da ya dace a matsayin masu kula da al’adunmu na gargajiya da samar da zaman lafiya tare da nesantar siyasar ɓangaranci.
Ana iya samun nasarar hakan ta hanyar tabbatar da ɗorewar ilimin al’umma, da tattaunawa da haɓaka mutunta waɗannan cibiyoyi masu daraja.
Yayin da muke kai-komo a cikin sarqaqiyar yanayin siyasar qasarmu, ka da mu manta da ximbin kima da muhimmancin da masarautunmu na gargajiya suke da su.
Ta hanyar kiyaye mutuncinsu da kuma kare su daga mummunar tasirin siyasar ɓangaranci, za mu iya tabbatar da cewa waɗannanasarautun sun ci gaba da zama ginshiƙan samun kyakkyawan fata da kuma kwanciyar hankali ga zurriyyar da ake hayayyafa.