Gwamnatin tarayya ta ce, yanzu haka dai kasashen Afrika da dama na tururuwan zuwa Nijeriya domin samun makaman da ake kerawa na sojoji na zamani.
Makaman wadanda ake kerawa a masana’antar tsaro ta Nijeriya (DICON), kamar yadda ministan tsaro, Bello Matawalle ya shaida, ya ce, wannan na nuni da irin azama da kwazon da ma’aikatar tsaro ta Nijeriya ke sanyawa da kuma sabbin jagororin hukumar DICON ke yi a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
- Dalilan Da Suka Sabbaba Karancin Abinci A Nijeriya — Masana
- Gwamnan Kano Ya Naɗa Shugaban Sabuwar Ma’aikatar Tsaro
Matawalle ya kara da cewa sayen makamai da kasashen Afrika ke zuwa Nijeriya, zai taimaka wajen bunkasa musayar da kudaden kasashen waje da ake samu a Nijeriya, kana zai samar da karin damarmakin ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya da kuma rage yawan ta’addanci.
Ministan ya shaida wa ‘yan jarida hakan a yayin bikin cikar shekara 60 na masana’antar kera makamai ta Nijeriya DICON, cewa sama da ‘yan kasashen waje 150 ne za su baji kolin fasaharsu da gogewarsu a yayin taron masana’antun tsaro na Afrika da kukuma baje kolin fasaha a Abuja.
Matawalle ya ce, “Lokacin da muka amshi ragamar jagorancin ma’aikatar tsaro, mun tashi tsaye wajen tabbatar da cewa DICON ta dawo ta tsaya kan kafafunta ta hanyar amfani da damarta wajen ganin muma a matakinmu muna kera makamai wanda hakan zai ba mu damar janyo hankalin masu zuba jari.
“Yanzu, kasashe da dama, ba kawai gwamnati ba, suna hada gwiwa da wannan masana’antar wajen kera makamai na soji na kimiyyar zamani.
“Ina tabbatar muku nan da lokaci kankani za ku ga irin kokarin da DICON ke yi wajen kera abubuwa da dama. Ba za mu fada irin karfinmu da abun da za mu iya yi ba, saboda dalilai na tsaro. Amma zan tabbatar muku cewa muna da nagarta kuma muna da karfin iya kera makamai, kasashen Afrika da dama suna zuwa Nijeriya domin siyan bindigogi da alburusai.”