Gwamna Abba Kabir Yusuf, na jihar Kano ya bayar da umarnin rusa wasu haramtattun gine-gine da aka gina a wasu wuraren da gwamnati.
Idan zaku iya tuna cewa, a cikin alkawuran yakin neman zabensa, ya bayar da tabbacin cewa zai dawo da martabar jihar ta hanyar kwato duk wani fili na jama’a da aka yi amfani da shi wajen kafa haramtattun gine-gine na mutane ko kungiyoyi.
- Abba Gida-Gida Ya Jagoranci Rusa Wani Gini Mai Hawa 3 Dauke Da Shaguna 90 A Kano
- Gwamnan Abba Gida-gida Ya Rushe Duk Nade-nade, Ya Kwace Duk Kadarorin Gwamnati Da Ganduje Ya Sayar
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce za a ruguza gine-ginen da aka gina a makarantu da masallaci da filin wasa da makabartu da kasuwanni da asibitoci domin tabbatar da bin ka’idar tsarin birane da kare lafiyar jama’a.
“Wadannan wuraren ana amfani da su ne don amfanin jama’a, don haka abin takaici ne ganin yadda ‘yan kasa marasa kishin kasa ke amfani da su”
A safiyar ranar Asabar dinnan, an aiwatar da rushe gine-ginen da ke filin wasan dawaki don kwato filin da aka yi amfani da shi ta haramtacciyar hanya.”
Muna kira ga al’umar Kano da su kara hakuri domin gwamnati mai ci ta himmatu wajen ganin Kano ta samu ci gaba, cewar gwamnan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp