Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, ya nemi a gurfanar da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Abbas, a kotu, bisa zarginsa da amfani da kalaman tada tarzoma.
Dan takarar, a karar mai lamba FHC/KN/CS/02/2023 da lauyansa Bashir Tudunwazirchi ya shigar, ya bukaci babbar kotun da ta gaggauta tilasta wa kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano ya binciki shugaban jam’iyyar APC tare da gurfanar da shi gaban kuliya.
- Sin Za Ta Ci Gaba Da Yin Mu’amalar Fasahohi Tare Da Hukumar WHO
- Kayayyakin Aikin Jarida Mafi Burgewa A Shekarar 2022: Gasar Wasannin Olympics Ta Lokacin Sanyi Ta Beijing Ta Kai Matsayi Na Farko
“Yana amfani da kalamomi wanda za su iya haifar da tashin hankali na siyasa a jihar nan”.
Sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun dan takarar, Sanusi Dawakin Tofa, ta ce dan takarar gwamnan na NNPP, ya garzaya kotu da nufin tunatar da ‘yan sanda su yi abin da ya kamata.
“Mun rubuta korafe-korafe da dama tare da kwararan hujjoji kan yawan ta’asar da shugaban jam’iyyar APC ke yi, amma har yau rundunar ‘yan sanda a Kano ba ta yi wani abu a kai ba.
“A ‘yan kwanakin nan, Abdullahi Abbas da dansa Sani Abdullahi Abbas da wasu makusantansa ne suka kai hare-hare da tashe-tashen hankula na siyasa, inda aka raunata wasu da ba su ji ba ba su gani ba, aka tsoratar da su amma duk da haka, ‘yan sanda sun gaza yin komai kan lamarin ,” in ji sanarwar.
Idan har kotu ta amince da koken nasa, hakan zai tilastawa rundunar ‘yan sandan Kano damke Abdullahi Abbas kan zargin kalaman nuna kiyayya, cin zarafi da kuma daukar nauyin ‘yan bangar siyasa.
Ana zargin Abdullahi Abbas da yin kaurin suna wajen amfani da kalaman batanci da wadanda ba su dace ba a siyasa.