Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sake nada Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin shugaban Hukumar Hisbah ta jihar karo na uku.
A baya dai, Sheikh Daurawa ya taba jagorantar hukumar har sau biyu, a zamanin mulkin tsohon Gwamnan Jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma farkon mulkin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
- Fisinjoji 20 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Hanyar Legas
- NiMet Ta Yi Hasashen Samun Zazzafar Rana A Gobe Talata A Jihohin Kano, Katsina Da Sokoto
Sai dai a shekara ta 2018, Daurawa ya sanar da ajiye mukamin lokacin da aka samu sabani tsakanin Kwankwaso da Ganduje.
Amma a ranar Litinin, malamin ya wallafa wani bidiyo da ya nuna shi yana karbar takardar sake nada shi shugabancin hukumar a karo na uku, daga Sakataren Gwamnatin Jihar, Dokta Baffa Abdullahi Bichi.
Ana ganin malamin ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar gwamnatin Jihar mai ci ta jam’iyyar NNPP.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp