Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da sabbin naɗe-naɗe domin bunƙasa manyan cibiyoyi da kuma inganta aikin gwamnati a faɗin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a, an bayyana cewa Dr. Bashir A. Muzakkar shi ne sabon Darakta Janar na Hukumar Kula da Fasahar Sadarwa da Zamani ta Kano (KASITDA), yayin da Kabiru Saidu Dakata zai shugabanci Hukumar Tallace-tallace ta Jihar Kano (KASA).
- ’Yansanda Sun Kama ’Yan Bindiga 17 Tare Da Kashe 3 A Abuja
- Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha
Dr. Fatima Abdul Abubakar (Amneef) ta zama Darakta Janar ta Hukumar KASPA.
Sauran da aka naɗa sun haɗa da Injiniya Isyaku Umar Kwa a matsayin Mataimakin Manajan Darakta na Hukumar Gidaje ta Jihar Kano, Hamisu Musa Gambo Danzaki a matsayin Sakataren Zartarwa na Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Kano.
Barrista Isma’il Nasarawa a matsayin Babban Jami’i a Cibiyar Yaƙi da Cin Hanci, da Kyaftin Mohd Bello Maigaskiya Gabasawa (mai ritaya) a matsayin Kwamandan Cibiyar Tsaron Cikin Gida.
Gwamna Abba ya bayyana gamsuwarsa da ƙwarewar sabbin jami’an da aka naɗa, inda ya bayyana cewa za su taka rawar gani wajen aiwatar da manufofin gwamnatinsa.
Ya ce jajircewa da ƙwarewarsu na daga cikin dalilan da suka sa aka zaɓe su domin su taimaka wajen ci gaban Jihar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp