Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi wani jawabi mai taken “gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tare” a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin Geneva a ranar 18 ga watan Janairun shekara ta 2017, wanda ya samu martani sosai a duk fadin duniya. Kuma jawabin Xi ya burge wani dan kasar Somaliya mai suna Abdilahi Ismail Abdilahi kwarai da gaske.
Abdilahi Ismail Abdilahi, malami ne dake koyarwa a jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing (BFSU) a halin yanzu, ya ce har yanzu ya tuna wata magana a cikin jawabin Xi, wato “babu wanda yake son yin gudun hijira, sai dai in an tilasta shi barin muhallinsa”. Ya ce wannan magana ta sa ya tuna tarihin gudun hijira da ‘yan Somaliya suka yi na tsawon lokaci, kuma yana kara fahimtar muhimmancin samun zaman lafiya da tsaro.
- Xi Jinping Ya Bukaci Hukumomin Shari’a A Kasar Su Karfafa Farfadowar Kasar Sin
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Yaba Da Abota Da Goyon Bayan Juna Da Togo
A jawabinsa na murnar shiga sabuwar shekara ta 2024, Xi ya ce, “muna son yin kokari tare da kasa da kasa don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da kara raya duniya mai kyau, bisa la’akari da makomar daukacin bil’adama da alfanunsu.”
Ismail ya taba ziyartar wurin da Xi Jinping ya yi aiki a lokacin kuruciyarsa, inda ya ce, har kullum shugaba Xi yana maida muradun al’umma a gaban komai, saboda ya taba zama cikinsu. Ya ce, “Da na ga shugaba Xi ya sha hannu da tsoffi, na tuna rayuwata tare da kakana a lokacin da nake karami. Shugaba Xi ya yi kama da manyanmu.”
A shekara ta 2021, Ismail da wasu wakilan matasa ‘yan kasashen waje sama da 30 sun gabatar da wani sako ga shugaba Xi Jinping. Ya ce, da zarar ya ga sakon da shugaba Xi ya rubuto musu, ya fahimci yadda yake kula da kowa dake zaune a kasar Sin. Ya ce, “Akwai wani karin magana a kasar Somaliya dake cewa, duk wanda ya san matsala, shi ne zai iya warware ta.” (Murtala Zhang)