….Ci gaba daga makon jiya
Duk wanda Allah ya bai wa wadatar arziki bai taimaki kowa ba, arzikin zai jefa shi hali makaskanci, babu mai kallonsa a duniya da lahira sabida bai taimaki mabukata ba.
Sabida haka, wanda ya ce, Talauci ya fi Arziki, ya yi amfani ne da halin kaskanci da dukiyar da ba a taimako da ita ke jefa mai ita. Mutum yana da dukiya, bai ci a cikinsa ba, bai taimaka wa kowa ba, dukiyar sai ta jawo wa ma’abocinta kaskanci a wurin mutanen duniya da bayin Allah. Don haka, a irin wannan hali ne, wanda ya ce Talauci ya fi arziki ya samu hujja. Wanda ya ce kudi ya fi talauci kuma, ya fada ne don kudin su zamar masa tsani wurin biyan bukatunsa na yau da kullum kuma su bashi aminci da nutsuwa wurin bauta wa Allah. Amma ba wai ya zama dan dakon kudin kawai ba, sai don su zamar masa tsani.
- Dakarun MNJTF Sun Daƙile Harin Da Aka Kai Sansanin Su, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 10 A Kamaru
- Sokoto Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan 15 Ga Gyaran Makarantu, Motocin Alkalai Da Sauransu
Duk wanda ya tara kudi bai fuskantar da su ta inda suka dace ba, zai zama kamar bai tara komai ba, sabida shi kanshi bai ci ba, bai yi aikin alheri da su ba, don haka Allah sai ya tambaye shi a duk lissafin kudin.
Mai ciyarwa, shi mai kudi ne da yawa, mawadaci ne, sabida tabbatarwarsa da amfanin kudin, ya taimaki mutanen duniya da bayin Allah da kudin, to wannan ko kudin sun kare, yana nan mawadaci kuma abun yabo a duk wurin halitta.
Daga Allah, zai kawo wani ya taimaka masa, sabida taimakon da ya yi lokacin yana cikin wadata. Allah ne da kansa zai nuna masa irin ikon sa, sabida taimakon da ya yi lokacin yana cikin wadata yanzun kuma babu, to sai Allah ya yi ta kawo masa masu taimakonsa. Sayyada Khadijah ita ta fara gwada irin wannan, ita ta fara ciyar da dukiyarta a Musulunci har sai da ta kare.
An tambayi Shehu Ibrahi Inyass kan almubazzaranci, mai tambaya yana cewa, Wai Shehu mene ne almubazzaranci? Shehu ya ce kashe Kobo a inda bai dace ba, shi ne Almubazzaranci amma ka ba da dukiyarka gabaki daya a inda ya dace, ba ka yi almubazzaranci ba. Sayyadina Abubakrus Siddik, ya ciyar da dukiyarshi gaba daya kuma Annabi (SAW) bai ce masa ya yi almubazzaranci ba. Hakan ta faru ne a yayin tattara kudade zuwa yakin Tabuka, Sayyadina Abubakar, gaba daya dukiyarsa ya kawo wa Annabi (SAW), ya ce ya bar wa iyalinshi Allah da Annabinsa (SAW).
Ga yabon da Allah ya yi masa a Alkur’ani har lahira, “Allazi yu’uti malahu yatazakka, wama li’ahadin indahu min ni’imatin tujza, illabtiga’a wajhi rabbihil a’ala, walasaufa yarda” wannan da ya kawo dukiyarsa don zatin Allah, ba ya bukatar kowa ya biya shi, ya yi ne kawai don neman yardar Ubangijinsa madaukaki, don haka, Ubangiji ya yi rantsuwa shi kuma zai saka masa da mafificin abinda ya ciyar har sai ya yarda (Sayyadina Abubakar).
Akwai Sayyada Khadijah, ita ta fara ciyar da dukiyarta gaba daya don taimakon addinin Allah, a karshen rayuwa, sai a Allah ya aiko yana gaishe ta kuma ya gina mata gida na Lu’u’lu’u a gidan Aljannah, don haka a ranar Alkiyamah, gidanta kawai za a yi ta fada, sabida kyawunsa.
Don haka, dukiya tana karewa amma Allah baya karewa.
Sabida haka, muka fahimci cewa, darajar kudi ba ta cikin yawan tara ta, tana cikin abin da aka yi da dukiyar ne. Wanda kudin suka zo masa, ya yi aiki da su, kudin sun zaman masa alkairi wanda kuma ya ki amfani da su, sun zaman masa kaskanci.
Mu tambayi kanmu, ya Annabi (SAW) ya yi da kudi, an bashi taskokin kasa gabaki daya, an bude masa garuruwa baki daya: Makkah da Madina da Siriya da Sham da Jaziral Larabawa baki daya da Hijaz. Sarakunan duniya suka tsorata da Annabi (SAW) suka dinga turo kyaututtuka kala-kala da yawa, aka halasta masa ganimar yaki, sabanin sauran Manzonnin kafin shi.
Duk garin da aka bude, sai an kawo masa daya cikin biyar na ganimar abin da aka samu, wadanda suka ki Musulunta kuma aka dora musu jizya, musulmai kuma suka dinga ba da zakkah. Babu wani sarki da aka tara ma wadannan abubuwan, kuma duk masu bayarda kudaden, suna bayarwa ne da yardar zuciyarsu ba da zalunci ba.
Duk wadannan ganima da jizya da zakkah duk Annabi (SAW) bai mallaki wani abu ba, ya ce wannan nasa ne. Duk abin da ya zo wurin Annabi (SAW) na kudi bai mallaki ko taro ba face ya bayar da shi. Ya ba wa baffansa, Abbas damar kwasan kudin zakkah iya karfinsa lokacin da aka samu kudi masu yawa daga Bahrain, ya ba wa Abu Sufyan Rakuma 100, ya azurta wasu da dama, ya karfafi musulmai.
An rawaito Annabi (SAW) yana cewa: “Ba ya burge ni, a ce ina da zinari kamar dutsen Uhudu amma a ce in kwana da zinari daya a wurina sai dai wanda zan ajiye don biyan bashi.”
Annabi (SAW) bai bar wa ‘ya’yan gidansa komai ba na daga dukiya, ya bar musu Allah da Manzon sa, shi ya sa duk inda Ahlul baiti suke, ake hada musu kudi na hadiyya sabida kakansu bai bar musu ba.
Burgewa ce, ka raya ‘ya’yan mutane, kai ma Allah zai kawo masu kula da naka bayan ba ka nan. Babu wata burgewa ka raya ‘ya’yanka ka kyale na jama’a.
Shehu Tijjani Abul Abbas ya kashe dukiya mai yawa kan ciyar da addini amma bai bar wa ‘ya’yansa dukiya ba, har gidansa ma na birni sai da ya siyar.
Ya ishe ka sanin waye Shehu Ibrahim Inyass, a wasiyyarsa ta rasuwa, ya rubuta wa ‘ya’yansa cewa, in za su iya saida littattafansa su siyar, in kuma sun yi hakuri ya roki Allah ya wadata su.
Don haka, Alhamdu lillah, hanyar Annbawa ga ta a fili – ciyarwa da kyauta; hanyar ‘yan duniya kuwa, ita ma a fili take – rowa.
Wata rana wasu kudade masu yawa sun zo wa Annabi (SAW) daga Bahraini, bayan ya raba kudaden sai Dirhami shida suka rage babu wanda za a bama wa, sai Annabi (SAW) ya bai wa daya daga cikin iyalansa ta rike kafin a samu wanda za a bai wa, Annabi (SAW) ya yi bacci ya zo, bacci ya ki zuwa, sai Annabi (SAW) ya ce wannan Dirhami shidan a fita da su, su suka hana shi bacci. Ana bayar da su sai Annabi (SAW) ya ce yanzu na huta, a wata ruwaya, Matan Annabi (SAW) sun ce, Annabi (SAW) ya yi bacci har ana jin minsharinsa.
Ya zo cikin ruwaya, Annabi (SAW) ya rasu rigar yakinsa tana wurin jingina a hannun wanda ba musulmi ba. Bayan rasuwar Annabi (SAW) sai wanda ke rike da rigar yakin ya ce, rigar yakin Annabi (SAW) tana hannuna, ya amshi kwanon alkama Talatin a hannuna sabida ciyar da iyalinshi. Sai Sahabbai suka biya shi kudin kwanon alkama Talatin suka amsa rigar sulken.
Manzon Allah (SAW), ya takaita cikin abincinshi da tufatinsa da wurin kwanansa a kan abin da ya zama darurar rayuwarsa (abin da dole ne da su za a rayu).
Kudi in zaka iya ajiye su a inda ya dace, ya zama alkairi amma akasin haka sai tara kudin ya zama sharri.