A wani yunƙuri na kawo ƙarshen ta’addanci, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatin sa na haɗa kai da hukumomin tsaro da suka haɗa da Cibiyar Nazarin Tsaro ta Ƙasa (NISS) don magance matsalar rashin tsaro a Jihar Zamfara.
A ranar Larabar da ta gabata ne tawagar manyan jami’ai masu karatun harkar tsaro na sirri ta ƙasa (EIMC) 17/2024 da jami’an na Cibiyar Nazarin Tsaro ta Ƙasa suka ziyarci Jihar Zamfara inda suka gana da Gwamna Dauda Lawal.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa, taken taron shi ne “Ƙirƙirarriyar Basira ‘IA’, Tsaro da Haɓaka Tattalin Arziki A Afrika: Ƙalubale Da Samar Da Mafita” Mahalarta taron sun fito ne daga hukumomi daban-daban a ciki da wajen ƙasar nan.
Sanarwar ta ƙara da cewa, taron ya baiwa mahalarta damar musayar ra’ayoyi da shawarwari kan batutuwa masu muhimmanci da mabambantan ra’ayoyi, wanda zai haifar da sakamako mai kyau.
Da yake jawabi ga jami’ai da mahalarta taron, Gwamna Lawal ya yaba wa cibiyar da ta zaɓi Jihar Zamfara domin gudanar da taron. “Shawarar ta dace ga wasu muhimman canje-canje da muke ƙoƙarin aiwatarwa. Kamar sauran sassan Nijeriya, Jihar mu tana da ɗimbin albarkatun ƙasa da na Ɗan’adam, waɗanda a matsayinsu na ginshiƙan ci gaban tattalin arziki, za su iya buɗe hanyoyin haɓaka tattalin arziki.
“Komawa kan maƙasudin taron tare da mai da hankali kan aikin Ƙirƙirarriyar Basira ta AI, gami da sabbin aikace-aikacen fasaha na Ƙirƙirarriyar Basira don haɓaka fa’idojin ma’adanai da ke cikin jiharmu da kuma magance barazanar da ke tattare da mu, dole ne mu daidaita su. Sanin wannan, gwamnatina tana aiki tare da hukumomin tsaro da sauran abokan haɗin gwiwa don haɓaka ƙwarewa a fannin fasaha don magance matsalolinmu.
“Saboda haka ina kira gare ku, mahalarta kwas ɗin, da ku yi tambayoyi da yawa tare da yin nazarin al’amuran da ke faruwa tare da samar mana da ingantattun shawarwari da suka dace da gwamnatin jiha don aiwatarwa. Idan har aka samu hakan, wannan ziyarar karatu za ta yi amfani matuƙa.”
Bugu da ƙari, Gwamna Lawal ya ƙara jaddada cewa gwamnatin jihar Zamfara na haɗa kai da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin daƙile barazanar tsaro.
“Tun da muka karɓi mulki kimanin shekara guda da ta wuce, mun ɓullo da wasu matakai na musamman da suka haɗa da tarukan Majalisar Tsaron Jihohi na yau da kullum don duba yanayin tsaro, da fara tsarin aiwatar da shi, da kuma kafa Asusun Tallafa wa Tsaro na Jihar Zamfara.
“Har ila yau, mun tsaurara matakai inda muka aiwatar da dokar hana zirga-zirga a kan takamaiman ayyukan da ka iya taimaka wa rashin tsaro a cikin Jihar; Ƙaddamar da Dokar Zartarwa da ta haramta wa sarakunan gargajiya bayar da izinin haƙar ma’adinai a cikin ƙananan hukumomi goma sha huɗu na jihar, don mayar da martani ga ƙaƙƙarfan alaƙar da ke tsakanin ‘yan bindiga da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
“Sanya dokar ta-ɓaci a harkokin lafiya da ilimi don mu samar da ci gaba mai amfani ga jama’ar mu cikin gaggawa a waɗannan fannoni, tare da shinfiɗa turbar samar da gobe mai kyau ga al’ummar jihar mu; Samar da rundunar tsaro ta musamman ta Askarawan Zamfara domin taimaka wa jami’an tsaron da ke jihar wajen shawo kan matsalolin tsaro ya addab.
Tun farko a nata jawabin, Shugabar tawagar jami’an daga wannan cibiya ta koyon harkokin tsaro, Madam Patricia Edak, ta yaba wa Gwamna Dauda Lawal ne bisa irin ci gaban da ya samar wa jihar a mulkin sa.
Ta ce, “Mai girma Gwamna, mun zagaya jihar nan mun ga irin manya-manyan gyare-gyare da ci gaban da ka samar a wannan ɗan ƙanƙanin lokacin da ka yi a kan mulki. Gaskiyar magana, jihar Zamfara ta yi gagarumar sa’a na samun ka a matsayin Gwamna.