Assalamu Alaikum Warahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu. Jama’a kar dai ku manta, wannan fili ne na musamman wanda yake kara tunatarwa tare da ankarar da sauran al’umma baki- daya game da wasu abubuwa; wadanda suke yawan ci mana tuwo a kwarya.
Kamar kowane mako, yau ma ina tafe da wani maudu’in da zan yi magana a kansa, wanda ya shafi fid da zakkah da kuma sa-daka, musamman a wannan lokaci da muke ciki na watan Ramadan.
- Turmutsitsin Rabon Tallafi Da Zakka: Yadda Mutum 10 Suka Rasu A Bauchi Da Nasarawa
- Da Gaske Babu Zakka A Cikin Dukiyar Da Aka Tara Ta Hanyar Haram?
Idan muka waiwaya, za mu ga cewa har yanzu a cikin al’ummar musulmai akwai mutanen da ba sa iya dora girki; bayan an sha ruwa, duk da cewa kusan koda-yaushe ana ta yadawa soshiyal midiya; game da yadda ake ta rabon kayan abincin wannan azumi.
Sai dai a nan, ni kiran da zan yi ga masu hannu da shuni shi ne, zakkar da ake fitarwa ta Naira 2000 ko Naira 3000, ba zakka ba ce, abin da ya kamata a yi shi ne; su rika waiwayawa suna duba wadanda ya kamata ko suka dace a bai wa wannnan zakkah ko sadaka.
Ba wai a rika yi kamar yadda ake yi a yanzu ba, me kudi ya dauki zakkah ya kai wa ‘ya’yan abokinsa mai kudi, shi ma in ya tashi fid da tasa zakkar, sai shi ma ya dauko ya kai wa abokin nasa, ya kamata a lura da cewa; wannan kyauta ce ba zakka ba.
Saboda haka, kada dai a manta akwai mutanen da suke fama da yunwa, abincin ma da za su ci gagararsu yake, kunun da za su karba a wannan watan azumin; za a ga mutum da yamma yana yawo da kwanon kunun da zai samo, wani ma har sai an sha ruwa ba tare da ya samo komai ba, wani kuwa iya kunun ne kadai zai sha.
Sannan, har yanzu fa akwai mutanen da ba sa iya shan ruwa a gidansu, har sai sun fito wajen mutane za su samu su sha ruwa saboda rashi, iyali kuma dan abin da aka samu na kunun sa-dakar nan; shi ne dai za a sha ruwa da shi, don haka wadannan su ya kamata a ba wa zakkah, kuma su ya kamata a bai wa sadaka.
Har ila yau, mukan manta da irin matsalolin da ake fuskanta; wanda ba komai ba ne, face irin wannan zakka wadda ake yi, saboda haka; ya kamata masu kudi su waiwayi wannan al’amari tsakaninsu da Allah, haka nan matan masu kudi, domin wan-nan jan hankali ne.
Haka zalika, abin dubawa a nan shi ne; irin wadannan abu-buwan su ne masifar, su ne halin da ake ciki na wannan matsa-la da ake fama da ita na kuncin rayuwa, watan azumi ne kuma watan ibada, sannan kuma lokacin da ya kamata a ce mun samu lada, lokacin ne na neman gafarar ubangiji, lokaci ne na neman kusanci ga ubangiji, saboda haka mu waiwayi irin wadannan mutanen, domin su ne wadanda idan ka ba su; ka sauke farilla, za kuma ka samu lada; ba wai ka rika yin zakkah zuwa zakkah ba, idan abokinka mai kudi ya ba ka, kai ma sai ka mayar masa da ita, don Allah mu yi kokarin yi domin Allah.
Ku sani cewa, duk wani mai kudi in dai har yana so dukiyarsa ta ci gaba da habaka, kar ya ce idan ya ciri wani abu a dukiyarsa za ta ragu. Don haka, idan ka fitar da wannan zakkah; kamar ka fid da hakkin Allah ne, a daure a cije a yi wannan, sannan kuma a bayar da sadaka don girman Allah, a yi zakkah domin Allah, tunda zakkah ma da ake so ka bai wa mutumin da idan shekara ta dawo shi ma zai iya bayarwa, ba don komai ba saboda idan fa masu kudi ba su taimaki talakawa ba, kamar suna daba wa cikinsu wuka ne.
Saboda haka, idan har ka ce daga kai sai ‘ya’yanka ko ‘ya’yan abokanka masu kudi, to wadannan ‘ya’yan talakawan da ba ka taimakawa ba, idan suka shiga cikin wata masifa ko halin ha’ula’i; to fa kan ‘ya’yan naka za su dawo, domin ‘ya’yanka naka su ma suna fita, zai kuma kasance wata rana kai ma babu kai, don haka idan ‘ya’yan wasu suka lalace; kai ma kana ji kana gani akwai halin da za ka iya kai wa ba za ka iya taimakawa ba.
Sannan ka sani cewa, wadannan ‘ya’yan rashin tarbiyyarsu kai tsaye kan ‘ya’yanka zai dawo, domin ko makaranta ko kasuwa ko neman kudi ko yanayi na guri daya, lokacin da ‘ya’yanka za su shiga cikinsu, idan ba su samu tarbiyya ba kenan duk tarbiy-yar da ka yi wa naka ‘ya’yan, ta tashi a banza.
Don haka, don Allah don Annabi mu yi kokari mu kiyaye, domin irin wannan ne ake cewa, alhairi ba ya faduwa kasa banza, shi kuwa sharri dan aike ne; idan ka yi shi kanka zai dawo, idan ka taimaki dan makocinka kamar danka ka taimaka, ko yara ne ba sa zuwa makaranta a cikin unguwa, idan har ka-na da yadda za ka yi; ka yi kokari ka mayar da su, domin kuwa kai ma kana gyara goben ‘ya’yanka ne.
Ubangiji Allah ya sa mu dace, ya shirye mu baki-daya, amin.