Tawagar Super Eagles ta Nijeriya za ta kara da kasar Gabon a wasanta na gaba na neman tikitin zuwa gasar Kofin Duniya da za a buga a kasashen Amurka, Medico da Canada, wasan wanda za a buga a kasar Moroko ranar 13 ga watan Nuwamba zai zama sharar fage a wajen kasashen biyu, Nijeriya ta doke kasar Benin da ci 4-0 a wasan da suka buga a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom ranar Talata, wanda ya kasance wasa na karshe da kasar ta buga a cikin rukunin C inda ta kare a matsayi na biyu maki daya tsakaninta da Afirika Ta Kudu wadda ta kare a matsayi na 1.
Zakarun na Afrika har sau uku Nijeriya ta samu damar zuwa wasan Sili daya kwale bayan doke Jamhuriyar Benin, inda suka kare matsayi na biyu a rukuninsu na neman tikitin shiga gasar, ita kuma Gabon ta samu nasarar kasancewa cikin kasashen da za su buga wasannin Play Off bayan nasarar da ta yi akan kasar Burundi da ci 2-0, nasarar da Ibory Coast ta samu a kan Kenya ne ya kara taimaka wa Gabon din kammala wasannin rukuni a matsayi na biyu a rukunin F.
- An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza
- Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu
A daya bangaren kuma DR Congo ta lallasa Sudan da ci 1-0, inda ta zo ta biyu a bayan Senegal a rukunin B, yayin da Kamaru ta kare a matsayi na biyu a rukunin D, kasashen Nijeriya, Gabon, DR Congo da Kamaru ne suka samu damar kasancewa cikin kasashen da za su buga wasan Sili daya Kwale, domin samun wadda za ta kara da wata kasa a Nahiyar Turai wajen ganin sun samu tikitin zuwa gasar Kofin Duniya.
Za a gudanar da wasannin a kasar Morocco daga ranar 13 zuwa 16 ga watan Nuwamba, wanda zai kunshi Nijeriya da Gabon, sai kuma Kamaru da DR Congo, kasashen da suka yi nasara a wasan farko za su hadu da juna wasa na biyu domin fitar da zakara wanda zai buga wasa daya da wata kasa a Nahiyar Turai a watan Maris na shekarar 2026, dukkan wasannin za su kasance haduwa daya, sannan kuma za a iya karin mintuna 20 idan bukatar hakan ta taso (Edtra Time), ana sa ran hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta tabbatar da birane da wuraren da za su karbi bakuncin gasar a cikin kwanaki masu zuwa.
Yayin da kasashe 9 ne daga Afirika zuwa yanzu suka samu nasarar zuwa gasar Kofin Duniya, wasan na share fage na iya zama wata hanya da Afirika za ta samu karin wakilai daga Nahiyar wadanda za su samu tikitin zuwa gasar Kofin Duniya wadda kasashe 48 za su buga a shekarar 2026.
wasan na badi zai kasance Kofin Duniya na farko da kasashe fiye da 40 za su buga, kuma za a gudanar da shi a kasashe uku da suka hada da Amurka, Medico da Canada, a takaice Nijeriya na bukatar samun nasara a wasanni 3 da za ta buga a jere kafin samun damar zuwa gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026.