Nan da ‘yan kwanaki kadan za a fara yin noman rani na alkama, musamman a Jihohin Kano, Katsina, Kaduna, Bauchi, Taraba, Kebbi, Jigawa, Sokoto, Gombe da sauransu.
Tsohon Kwamishinan Ma’aikatar Aikin Noma na Jihar Gombe, kuma guda cikin manyan manoma, Alhaji Muhammad Magaji Gettado ya bayyana cewa, manoman da suka yi shuka bayan ranar 15 ga watan Nuwamba, za su iya samun matsala ko tangarda a gonakinsu.
 Sannan ya kuma yi kira ga Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, da ta tabbatar tana tallafa wa manoman alkama a kan lokaci, inda ya yi nuni da cewa, dabi’ar raba wa manona kayan aikin noma a makare ne ke jawo wa manoman kasar nan rashin samun amfani mai yawa bayan sun yi girbi.
Sai dai, wasu kwararru a fannin noman alkamar sun bai wa manoman kwarin guiwar cewa, za su iya yin shuka daga ranar 15 ga watan Nuwamba zuwa ranar 15 ga watan Disamba.
Kazalika, sun bayyana cewa; wadanda suke son su samu girbi mai yawa, za su iya yin shuka a makon farko na watan Nuwamba, ganin cewa alkama ta fi bukatar yanayin sanyi.
Daya daga cikin kwararru a wannan fanni kuma shugaban kungiyar masu sarrafa wa da kasuwancin alkama na kasa, Kwamanda Sojin Sama, mai ritaya Shuaibu Hamza ya sanar da cewa, kungiyar ta ware akalla kadada 77,000 domin yin noman alkama na rani.
Ya kara da cewa, a Jihar Neja akalla akwai kadadar yin noma kimanin 40,000, inda ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu manoman nata su kimanin 20,000 ne suka yi rijista, domin fara yin noman wannan alkama na rani.
Bugu da kari, a mako biyu da suka gabata ne, Ministan Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara da Samar da Wadataccen Abinci, Sanata Abubakar Kyari ya sanar da cewa, gwamnatin tarayya za ta noma kimanin kadada 70,000 a jihohin kasar nan da ke yin noman alkama, wadda ake sa ran za a samu girbin da ya kai na tan 875,000 domin adanawa.
Abubakar ya kara cewa, za a ware kadada 40,000 a Jihar Jigawa, sauran kadada 30,000 kuma za a raba su ga sauran jihohin da ke noman alkamar.
Wannan yana nuna cewa, Jihar Jigawa ita ce ta fi samun kaso mafi yawa, sakamakon jajircewar da take da shi a wannan fanni na noman alkamar, inda ta yi kokarin ware har kimanin kadada 40,000.