Duniya Ce Ta Gina Majalisar Dinkin Duniya, Domin Hidimta Wa Al’ummar Duniya.
Tun daga 1945, ya zama an tsara wasu kasashe da za su samar da mafita da hadin kai domin magance matsalolin duniya da samar da zaman lafiya.
Mafitar da za ta kawo sassaucin tashe-tashen hankula, da kuma gina hanyoyin da za su wanzar da zaman lafiya.
Ba wani abu ne mafita illa kawar da fatara, da zaburar da ci gaba mai dorewa, da tsayawa domin ganin an taimaki masu rauni.
Mafitar da ke ba da agajin ceton rai ga mutanen da ke rayuwa a yankunan da ke fama rikice-rikice, tashe-tashen hankala, matsalolin tattalin arziki da bala’o’in sauyin yanayi.
Mafitar da ke daidaita ma’aunin adalci da daidaito ga mata da ‘yan mata.
Hanyoyin da ke magance batutuwan da ba za su iya misaltuwa ba tun da 1945, canjin yanayi, fasahar dijital, basirar wucin gadi, da sararin samaniya.
A cikin Satumba, Babban Taro ya amince da Yarjejeniya domin ci gaban Ka’idar Dijital ta Duniya da Sanarwa kan Karni mai zuwa.
Wadannan muhimman yarjejeniyoyin za su taimaka wajen tabbatar da cewa tsarin Majalisar Dinkin Duniya ya daidaita gyare-gyare da sake sabuntawa, don haka ya dace da sauye-sauye da kalubalen da ke kewaye da mu da kuma samar da mafita ga kowa.
Amma aikinmu zai kasance a koyaushe mai tushe a cikin dabi’u da bin ka’idodin Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa, da kuma mutunta ‘yancin dan’Adam na kowane mutum.
A cikin duniya mai wahala a yau, har yanzu ba a cimma wannan burina ba
Fatanmu bukatar yunkurin aiki da hanyoyin magance rashin zaman lafiya, wadata juna da bunkasa duniya.
Burinmu shi ne, tabbatar da bukatar duk kasashe su yi aiki kafada-da kafada.
Wannan shi ne abin da Majalisar Dinkin Duniya ke bukata.
A wannan rana ta Majalisar Dinkin Duniya, ina kira ga dukkannin kasashe da su kiyaye wannan haske ga duniya, da manufofinta ke haskakawa.