• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Ya Sa Farashin Kayan Masarufi Ya Fadi Warwas A Nijeriya

by Abubakar Abba
3 years ago
Masarufi

Sakamakon sabon tsarin da babban bankin Nijeriya CBN na sauya  takardun kudi na naira 1,000 da naira 500 da kuma naira 200 ya jefa ‘yan kasuwa a cikin tsaka-maiwuya, inda suke ci gaba da koka wa, kan asarar da  karancin sabbin kudin suka janyo wa sana’o’insu.

Har ila yau, rahotannin sun bayyana cewa, hakan ya kuma janyo faduwar farashin kayan masarufi a kasuwanni sakamakon karancin takardun kudaden a sassan kasar.

  • NIS Ta Yi Wa Jami’ai Sama 60 Karin Girma
  • Matsafa Sun Kashe Tare Da Cire Sassan Jikin Wani Dalibi A Adamawa

Kusan wannan matsalar ta karade kowanne fannin tun daga fannin hatsi da kuma dabbobi.

Rahotanni sun bayyana cewa, farashin hatsi da sauran kayan abinci sun fadi warwas  a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano, inda dole ta sa ’yan kasuwar suka fitar da farashin kaya iri biyu farashin mai biya da tsabar kudi daban, na mai biya ta tura kudi.

A kasuwar ta Dawanau, bayanai sun nuna cewa,  babban buhun masara da ake sayarwa naira 22,000 a makon jiya ya koma naira 14,000 da tsabar kudi, ko kuma naira 18,000 ga mai biya yin turin kudi.

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Bugu da kari,  babban buhun gero da ke naira   25,000 a makon da ya wuce kuma ya koma naira 15,000 da tsabar kudi, ko naira 18,000 ga mai tura kudi,  inda kuma buhun shinkafa mai buntu mai nauyin 100 kilo  kuma ya koma naira 13,000 daga naira 23,000 da aka sayar a satin da ya gabata.

Wasu daga cikin masu hada-hadar hatsi a kasuwar sun bayyana cewa, a kan dole suke sayar da kaya, ko da faduwa za su yi don su samu abin da za su kula da iyalansu.

A cewarsu, rashin takardun kudi  ya sa kaya sun karye, ko ma ta wace hanya za a biya.

A jihar Kano a kasuwar kayan gwari ta ‘yankaba kuma, kwandon tumatir da ke naira 8,500 a makon jiya ya koma naira 4,000 saboda rashin ciniki.

A kasuwannin Jos da ke jihar Filato kuma farashin dankali, dankalin taurawa da sauran kayan gwari sun fadi  warwas, inda  kasuwar Farin Gada da ke Jos, kwandon tumatir da a baya ake sayarwa naira 1,500 zuwa naira 2,000 ya wuce ya koma naira I,  700.

Hakazalika, a kasuwar Maikatako, wadda ta yi fice wajen kasuwancin dankalin turawa a karamar hukumar Bokkos, farashin dankali ya fadi warwas, buhu mai nauyin kilo 50 na dankali ya koma naira 6,500 daga  farashinsa na naira 10,000.

A cewar wasu kananan manoma, mu ne muka fi shiga cikin matsala a wannan yanayi, inda suka kara da cewa, a makon da ya gabata a kasuwar kauyen Jamari an sayar da buhu mai nauyin kilo 100 na gero naira 7,000 sabanin naira 20,000 da ake sayarawa a baya.

A bangaren Masara ta koma naira 8,000-naira 10,000 amma kusan babu mai saya; Wake ya koma naira 19,000 daga naira 40,000; abin gwanin ban tausayi, kusan babu wanda bai shafa ba, saboda rashin takardun kudi.

Har ila yau, karancin kudin  ta sa rashin ciniki a kasuwar Alaba Rago da ke Jihar Legas, inda ’yan kasuwa ke ta korafi kan gazawar abokan cinikayya wajen samun tsabar kudi don yin sayayya.

A cewar wasu masu sana’ar sayar da kajin da aka sayar naira 10,000 a watan disamba da farkon watan janairu sun koma naira 6000, amma duk da haka babu mai saye.

Wasu ’yan kasuwa a kauyen Oke-Aro da ke kan iyakar jihohin Legas da Ogun sun bayyana irin asarar da suka tafka sakamakon rashin takardun kudaden.

Hakazalika, masu sana’ar sayar da kayan gwari a kasuwar Agbado don sayarwa a Oke-Aro ta bayyana cewa farashin kayan ba su canza ba, amma matsalar ita ce tashin farashin abin hawa, inda wasu tun da aka fara karancin takardun ba ya samun ciniki sosai.

A Jihar Kwara, wata ’yar kasuwa mai sayar da waken suya a  karamar hukumar   Kaiama, mai suna Amina ta ce lamarin ya sa ba su da zabi sai dai su koma su zauna a gida.

Wata mai sayar da hatsi mai suna Maimuna a Kaiama, ta ce ta bar sana’ar a halin yanzu saboda rashin uwar kudi  da kuma abin kula da  kanta.

A cewar wata  mai shinkafa da wake, Salamat, a Kasuwar Mandate da ke Ilorin ta ce duk da cewa ba asara suke yi a kayan da suke sayarwa ba, matsalar ta rage yanayin cininkinsu da ma harkar hatsi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
Noma Da Kiwo

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

November 2, 2025
Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya
Noma Da Kiwo

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Next Post
Benzema Da Mbappe Da Messi Suna Takarar Gwarzon Dan Kwallon FIFA

Benzema Da Mbappe Da Messi Suna Takarar Gwarzon Dan Kwallon FIFA

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

November 6, 2025
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato

November 6, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025

November 6, 2025
Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.