Fernando Reimers, wanda Daraktan ilimi ne a Jami’ar Harbard, sannan kuma mamba ne a hukumar UNESCO; a kan al’amuran da suka shafi fannin ilimi da kuma ci gabansa, an jiyo shi a wata tattauna da ya yi a CNBC yana cewa, muddin ba a tsaya an yi gyara a kan al’amuran da suka shafi ilimi ba, ko shakka babu akwai matsala a nan gaba.
Sai dai kuma, Bankin Duniya ya bayyana cewa; don mutum yana zuwa makaranta, ba shi ne yake nuna cewa; yana koyo ba (2019). Misali, kamar wanda ya karanta bayanin Likita ne ko kuma ya yarda cewa; mota za ta rika daukar fasinja, su ne dabarun abin da yawancin yara ba su samu damar sani ba.
- Zamfara Ta Zama Jiha Ta Farko Da Ta Ƙaddamar da Tsarin Ilimin Fasahar Zamani
- Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (3)
Me yasa ilimi yake da muhimmanci? Dabaru, ilimi da kuma kware ta mutum, ana samun su ne ta hanyar ilimi. Wani binciken da Bankin Duniya ya sa aka yi a shekarar (2018) ya nuna cewa; kashi 56 na yaran da aka haifa a duniya, na iya asaar kudaden da suka samu wadanda za su iya taimaka musu wajen tafiyar da rayuwarsu. Dalili kuwa shi ne, gwamnatocinsu ba su zuba jari an kula da lafiya, ilimi da kuma irin wureren ayyukan da za su iya yi a nan gaba ba.
Kamar yadda Bankin duniyar ya ce, a shekarar (2019), an samu matsalar koyo ne saboda yawancin makarantu a kasashe daban-daban na hannu baka- hannu kwarya, wadanda ba su da alkalumman wadanda suke karatu da wadanda ba sa yi. Shi yasa ba za su iya yin wani abu ba dangane da hakan.
Dalili kuwa, ba a san irin bukatun da ake da su ba na lamarin da ya shafi ayyuka, matsalar ita ce makarantu da Malaman makaranta, akwai bukatar su koya musu bangaren da ya shafi rubutu da karatu.
Kazalika, dalibai su kasance suna iya yin bayani a kan abin da suka fahimta na abin da aka koya musu, sannan su rika bayar da shawarwari, su kasance za su iya yin wani abu ta kirkira, su yi mu’amala da wasu ba tare da wata matsala ba, su ba da hadin kai, su kasance suna iya yin abin da ake so su yi.
Idan har aka samu damar magance wadannan matsaloli da aka ambata a sama tare kuma da tabbatar hanyoyin da ake bi koyarwa, ta haka za a iya samun gyaran da ake bukata.
Bankin duniya a shekarar (2019) ya ce, ana fara samun sauyi ne daga Malaman makaranta; wadanda suka san abin da suke yi da kuma irin salon da ake amfani da shi wajen koyarwa. Bugu da kari kuma, ya kamata masana ilimi su yi amfani da irin ci gaban da fasaha ta kawo a wannan fanni na koyarwa.
Wasu Abubuwa Da Suka Shafi Ilimi A Duniya
Kashi 88 na yara mata da kuma kashi 91 na yara maza, suna da ilimin Firamare, sai dai kuma mata da dama na samun ilimi mai zurfi fiye da maza, (World Economic Forum, 2019).
A shekarar 2020, yawancin wadanda suka kammala karatun Firamare a fadin duniya baki-daya, kashi 90.14 cikin 100 ne, (UNESCO, 2021e).
A cikin shekarar, an samu raguwar wadanda suka kammala karatun Sakandaren da kashi 77 cikin 100, (UNESCO, 2021d).
Haka nan ma, wadanda suka yi makarantar yaki da jahilci ‘yan shekara 15 da wadanda suka haura haka, kashi 86 ne cikin 100, (UNESCO, 2021c).
Wadanda suka yi yaki da jahilci ‘yan shekara 15 da wadanda suka haura haka, sun zarce kashi 83.3 cikin 100, yayin da su kuma maza suka kasance kashi 90 cikin 100, (UNESCO, 2021a; UNESCO, 2021b).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp