• English
  • Business News
Tuesday, October 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Ya Sa Manoman Katsina Suka Mayar Da Martani Kan Alkwarin Gwamna Radda

byAbubakar Abba
2 years ago
inNoma Da Kiwo
0
Abin Da Ya Sa Manoman Katsina Suka Mayar Da Martani Kan Alkwarin Gwamna Radda

Labarai Masu Nasaba

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

Wasu daga cikin manoma a jihar Katsina sun bayyana jin dadinsu akan furucin gwamnan jihar Dikko Umar Radda na farfado da fannin aikin noma da kuma kara habaka fannin tattalin arzikin jihar.

Manoma sun bayyana jin dadin na su ne, biyo bayan jawabin da Radda ya yi bayan a rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar a watan da ya wuce.

  • Hajjin Bana: NAHCON Ta Samar Da Biza 73,310, Tare Da Kai Alhazai 46,000 Kasar Saudiyya
  • Kungiya Ta Yaba Wa Shugaba Tinubu Kan Inganta Tsaro Da Yaki Da Rashawa

Radda, a jawabin na sa ya bara tabbacin cewa, gwamnatinsa za ta tabbatar da ta zuba jari a fannin, wanda hakan zai sa manoman jihar su samu ribar da ta kai ta sama da kashi 85.

Bugu da kari, ya kuma yi alkawarin kara bunkasa fannin tattalin arzikin jihar.

Daya daga cikin manoman da ke noman Masara Alhaji Wada Isah a karamar hukumar Dandume ya bayyana cewa, ya kamata gwamntin jihar ta janyo manoman jihar wajen wanzar da tsare-tsare da kuma shirye-shiryen da ta zo da su don a samu nasara wajen habaka fanin.

Sun yi nuni da cewa, ganin cewa Radda shi ma manomi ne da kuma irin kokarin da ya yi a lokacin da yake rike da shugabancin hukuar  SMEDAN, muna da yakinin cewa, zai iya samar da sauyi a fannin aikin noman jihar.

“Ya kamata gwamntin jihar ta janyo manoman jihar wajen wanzar da tsare-tsare da kuma shirye-shiryen da ta zo da su don a samu nasara wajen habaka fanin.”

Ya sanar da cewa, babban abinda ya fi ci masu Tuwo a Kwarya shine tsadar Takin zamani, magungunan feshi da sauransu.

Shi ma wani manomin da ke a karamar hukumar Faskari Habibu Garba ya bayyana cewa,  kara habaka yin noma don samun riba, musaman noman Waken Soya, Alkama da kuma Masar, hakan zai kara habaka fannin aikin noma na jihar da kuma kara samar da ayyukan yi, musamman a tsakanin matasa.

A cewar Habibu, samar wa da moman jihar rumbun adana amfanin noma da suka girbe, musamman Tumatir da Albasa, Dankalin turawa, musamman don su rage asarar da suke yi .

“Kara habaka yin noma don samun riba, musaman noman Waken Soya, Alkama da kuma Masar, hakan zai kara habaka fannin aikin noma na jihar da kuma kara samar da ayyukan yi, musamman a tsakanin matasa.”

Habibu ya kara cewa, manoman sun shafe shekaru da dama suna burin a samar masu da Rubun adana amfanin gonakansu da suka noma.

Ya sanar da kara fadada noman Dankalin turawa a jihar, musamman a karamar hukumar  Bakori na da banna mahimmanci ba a karamar hukumar kawai ba, har da a fadin jihar .

“Manoman sun shafe shekaru da dama suna burin a samar masu da Rubun adana amfanin gonakansu da suka noma.”

Tags: KatsinaManomaRadda
ShareTweetSendShare
Abubakar Abba

Abubakar Abba

Related

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

4 days ago
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

4 days ago
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

1 week ago
Next Post
Mace Aba Ce Mai Daraja, Ba Sai Ta Ba Da Kanta Ba Za Ta Yi Suna A Fim – Jamila Saleh

Mace Aba Ce Mai Daraja, Ba Sai Ta Ba Da Kanta Ba Za Ta Yi Suna A Fim – Jamila Saleh

LABARAI MASU NASABA

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane

October 7, 2025
Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu

October 7, 2025
Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

Isra’ila Ta Kashe Falasɗinawa Sama Da 66,000 A Gaza Cikin Shekaru 2 – Rahoto

October 7, 2025
Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga

Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga

October 7, 2025
Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya

Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Da Zai Binciki Harkokin Kirifto Da POS A Nijeriya

October 7, 2025
Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

Ya Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa

October 7, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Rage Kuɗin Aikin Hajjin 2026

October 7, 2025
Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

Kotu Ta Aike Da Ɗan TikTok Gidan Gyaran Hali Kan Bidiyon Batsa A Kano

October 6, 2025
Kada Ku Yi Sanadiyar Rugujewar Matatar Mai Ta Dangote – Shettima Ga PENGASSAN 

Kada Ku Yi Sanadiyar Rugujewar Matatar Mai Ta Dangote – Shettima Ga PENGASSAN 

October 6, 2025
Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   

Habakar Yin Sayayya A Lokacin Hutu Ta Nuna Kirkira Da Irin Ci Gaban Da Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samu   

October 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.