Bincike ya nuna cewa, mata sun fi mazaje fuskantar barazanar yiwuwar kashe kansu saboda irin matsaloli na damuwa da suke fuskanta a rayuwar yau da kullum.
Wata fitacciyar Likitar kwakwalwa, Farfesa Aishatu Yusha’u Armiya’u ce ta bayyana haka a tattaunawarta da manema labarai jim kadan bayan sanar da nada ta Shugabar Asibitin Masu Tabin Kwakwalwa da ke Barnawa a Kaduna.
- Za Mu Taimaka PDP Ta Fadi Zaben 2023 -Wike
- Wasu Fusatattun Matasa Sun Afka Wa Tawagar Sanata Kwankwaso A Jihar Kogi
A ranar 18 ga watan Agusta 2022 Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Farfesa Aishatu Yusha’u Armiya’u (MBBS, Cert. LMIH/ FIS, PGDE, MSc, MBA, PhD, FMCPsych, FWACP, IFAPA, MNIM) a matsayin shugabar Asibitin Masu Cutar Kwakwalwa da ke Barnawa, Kaduna, wanda hakan ke nuna cewa, ita ce mace ta farko a fadin Arewacin Nijeriya da ta fara rike mukamin shugabancin Asibitin masu Tabin Kwakwalwa a fadin Arewacin Nijeriya.
Duk da cewa, Farfesa Aishatu Yusha’u Armiya’u ta taso ce daga Arewacin Nijeriya inda mata ba su cika samun damar zurfafa karatunsu na boko ba amma ta jajirce har ta samu kammala digirinta a fannin aikin likita a Jami’ar Bayero da ke Kano Nijeriya.
Ta kuma kasance Mamba na cibiyar kwararu ta ‘National Postgraduate Medical College of Nigeria (FMCPsych)’ da ‘West African College of Physician (FWACP)’.
Haka kuma Farfesa Aishatu ta kammala digirinta na biyu da yabo kyakyawa daga Jami’ar Liberpool da ke Landan inda ta kware fannin ‘Forensic Psychology and Criminal Inbestigation (MSc. FP&CI)’.
Farfesa Aishatu Armiya bata tsaya a nan ba don kuwa ta yi karatu na musamma a kan harkokin shugabanci da gudanarwa a Jami’ar Washington da ke kasar Amurka ta kuma yi babbar difloma a kan koyarwa daga Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara daga nan ta zarce Jami’ar Central De Nicaraguainda inda ta yi digirinta na Dakta wato digirin digirgir.
Ta kuma samu nasarra samun digirinta na biyu a fannin kasuwanci inda ta karkata kwarewar ta a kan hanyoyin tafiyar da kiwon lafiya da tafiyar da gudanar da asibitoci, ta kuma halarci tarurukan kwarruna a kan harkokin kiwon lafiya a ciki da wajen kasar nan.
Kafin nadata shugabar asibitin Masu Cutar Kwakwalwa na Barnawa Kaduna, ta yi aki a matsayin babbar Likitar kula da cututtukan kwakwalwa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tafawa Balewa da ke Bauchi tana kuma jagorantar likitoci masu sa ido a gidajen yarin Jos a jihar Filato.
Aishatu ce mace ta farko daga Arewa da ta samu wannan kwarewar a bangbare kula da cututtukar kwakwalwa a Nijeriya.
Ta bayar da gudummawa a fannoni da dama wajen bunkasa lafiyar al’umma a ciki da wajen kasar nan a tattaunawar ta farko bayan nadin da aka yi mat ana shugabar Asibitin Masu Cutar Kwakwalwa na Barnawa kaduna ta bayyana cewa, Mata Sun Fi Fuskantar Yiwuwar Kanshe Kan Su Fiye Da Maza, ga dai yadda tattaunawar ta kasance a rahoton da Wakilinmu ya fruwaito mana.
Wata shaharraiyar masanaiyar ilimin kwakwalwa, Farfesa Aishatu Yusha’u ta bayar da gamsashiyar dalilai da ke bayyana abubuwan da suke sanya mata suka fi fuskantar barazanar yiwuwar kashe kansu fiye da maza, musamman ganin sun fi fukantar matsaloli na damuwa fiye da takwarorinsu maza.
Farfesar ta bayyana haka ne a tataunawarta da manema labarai a a Kaduna, ta kuma kara da cewa, tsananin damuwa na haifar da kisan ka, damuwar da mata suka fi fuskanta sun hada da rashin kudi da matsalolin da suka shafi rayuwar zaman aure, kamar yadda binckike na bayabaya nan ya nuna.
Daga nan Farfesar ta kuma ce, an fi samun kisan kai a gidaje, makarantu, da masu fadawa cikin ruwa, an kuma fi samun mata da aikata irin wannan nau’io na kisan kai.
Ta ce, tabin hankali na daya daga cikin abubuwan da suke haifar da kisan ka da cikin al’umma.
Ta ce, “A kwai banbanci na yawan masu kashe kansu a tsakanin mata da maza, bincike ya nuna cewa, matsalolin rashin kudi da rikice-rikicen zaman aure na daga cikin dalilin da ke jefa mata kashe kansu, amma dalilan da ke jefa masa kashe kansu ya banbanta, a kan haka in ana son kawo karshen lamarin kisan kai dole a fuskance shi ta hanyar lura da banbanci a tsakanin mata da maza, don lamarin ba daidai ba ne a tsakannin maza da mata.
“A nawa ra’ayin yakamata gwamnati ta samar da kudade masu yawa don gudanar da bincike a cikin al’umma ta haka za mu samu cikakken hujjoji na sanin yadda za a kawo karshen wannan lamarin, a kan haka lamarin kula da lafiyar kwakwalwa ga al’umma ke da matukar muhuimanci a wuraren da suka hada mamakarantu gidaje da sauransu, ta haka be za a iya kamo hanyar kawo karshen yawaitar kisan kai a cikin al’umma” Farfesar ta kuma bayyana cewa, bincike ya nuna dole a fara daga gidaje ta hanyar amfani da iyaye da makwabta sannan a wuto makarantu don samar da hanyar kawo karshen wannan matsalar.