• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Abin Da Ya Sa Muka Gamsu Da Manufofin Kwankwaso – Matasan Arewa A Legas

by yahuzajere
3 years ago
Kwankwaso

Shugaban Gamayyar Matasan Arewa Mazauna Jihar Legas, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci ya bayyana cewa sun gamsu da manufofin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa yadda suka ƙunshi dabarun magance manyan matsalolin da suka addabi Nijeriya a zamanin nan.

A cewar Galadanci, lokaci ya yi da ‘Yan Nijeriya za su zabura su tabbatar da nagarta wajen zaɓen shugabannin da suka fi cancanta a zaɓen 2023 domin fita daga halin da suke ciki na rashin tsaro da tsadar rayuwa.

  • Shugaba Buhari Ya Gana Da Sarki Charles III Na Birtaniya A Landon

Ya ƙara da cewa, “Ƙungiyarmu ta Gamayyar Matasan Arewa a Legas, mun fahimci manufofin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso kuma mun gamsu da jawabinsa da ya yi wa al’ummar Nijeriya da ma duniya baki ɗaya. Abin da ya fi ɗaukar hankalinmu a jawabin nasa shi ne idan Allah ya ba su ikon cin nasara a zaɓen 2023, ya ƙudiri aniyar magance matsalolin tsaron cikin gida a Nijeriya da iyyakokinta, musamman ƙudirin da ya yi na zai ɗauki sojoji kimanin miliyan ɗaya da ‘yansanda miliyan ɗaya da sauran jami’an tsaro waɗanda za a tantance su tun daga matakin ƙaramar hukumarsu har zuwa jiha, yin hakan babbar nasara ce ga ƙasarmu da kuma ‘yan ƙasa baki ɗaya. Sannan da batun bunƙasa harkar ilimi da sauran tsare-tsare na alheri wanda waɗannan maganganu su ne suka ba mu damar mu taya su da addu’o’inmu na alheri a kan Allah ya cika musu burinsu mu samu zaman lafiya da ci gaban al’umma.

“Ƙasarmu mun san yadda Allah ya yi mata arzikin ma’adanai masu daraja waɗanda muna ji muna gani wasu na yi mana kisan gillah, suna amfani da wannan damar suna kwasar dukiyar. Sun haɗa baki da baƙin haure an hana mu zaman lafiya. Don haka wannan lokaci ne da za mu mu fito domin ganin an daina yi wa al’ummar Nijeriya wasan wawaso da dukiyar da Allah ya bayar ga ƙasar domin al’ummar Nijeriya su amfana. Ba kuɗi za a ba mu ba domin muna dimokraɗiyya ne a yanzu, ya kamata mu tashi tsaye mu kawo wa ƙasarmu ci gaban da za mu yi alfari da ita a matsayin Nijeriya ƙasa ɗaya mai al’umma ɗaya da ke samun bunƙasa.

“Muna kira ga ‘Yan Nijeriya a kan su fahimci cewa abin da muka fi buƙata a wannan zaɓen na 2023 da za a yi shi ne mu yi watsi da harkar ubangida, kowane ubangida yana da wani muradin kansa a fagen siyasa kuma wannan muradin ba don kishin ci gaban jama’a ba ne sai dai ci gaban kansa da iyalansa. Don haka wannan ne lokaci mafi dacewa da za mu yaƙi azzalimai waɗanda ana yi mana kisan gillah ba dare ba rana amma ba su damu ba, yadda za su ci gaba da mulki da ɗora nasu a kai kawai suke ƙoƙarin yi saboda sun mayar da mulkin ƙasar ya zama na gado.” In ji shi.

LABARAI MASU NASABA

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar

Ya ƙara da cewa, yadda aka riƙa sayen wakilai masu zaɓe tun daga zaɓen fitar da gwani, manuniya ce ta neman ƙara danne talakan Nijeriya.

“A idon duniya manyan ‘yan takara suka dinga sayen wakilai masu zaɓe da ake ce wa ‘delegate’ domin su ci gaba da kassara mu. Talakan Nijeriya ya san irin uƙubar da yake ciki. Don haka muna ƙara yin kira ga shugabannin manyan ƙasashe na duniya, matuƙar suna son ɗorewar dimokuraɗiyya a Nijeriya, su taimaka wajen tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya ne suka zaɓi waɗanda suka cancanta da za su fitar da su daga halin da ƙasar take ciki. Duk wani ɗan ƙasa nagari da ka sani ya gaji da kisan gilla da tsadar rayuwa. Mu a matsayinmu na gamayyar matasan arewa da ke Legas, muna kira ga dukkan ‘yan ƙasa ba tare da bambancin ƙabila ko addini ba, mu tashi tsaye mu zaɓi cancanta, wannan ne kaɗai zai kai mu ga tudun mun tsira a 2023.” Ya bayyana.

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
Manyan Labarai

Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna

November 1, 2025
Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
Siyasa

Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar

October 31, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato
Manyan Labarai

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
Next Post
A Shirye Kwankwaso Yake Ya Karbi Alasan Ado Doguwa A Kwankwasiyya —Rurum

Rikicin Doguwa Da Garo: Yadda Siyasar Kano Ta Dauki Sabon Salo

LABARAI MASU NASABA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su

November 2, 2025
Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.