- Mahangata Game Da Rabon Mukamai A Gwamnatin
- Zan Fara Da Tunatar Da Gwamnati Halin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki
- Za Mu Sa Ido Mu Ga Inda Ya Kamata A Gyara
- Ba Ni Da Matsala Da Ɗan’uwana Na Jam’iyyar LP
A farkon makon nan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa ta “Northern Elders Forum”, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, a matsayin Mai Bai Wa Mataimakin Shugaban Kasa Shawara A Kan Harkokin Siyasa. Malamin jami’a, Dakta Hakeem kwararre ne a kan harkokin zamantakewar al’umma wanda ya kasance mai rajin kare hakkin Arewacin Nijeriya da Dan’arewa a bangarori daban-daban. A wata hira da ya yi da Editanmu, Abdulrazak Yahuza Jere ta wayar tarho, ya bayyana mahangarsa kan ce-ceku-cen da ake na yadda Tinubu ya Fifita yarbawa wajen bayar da mukamai masu maiko, kana da dalilansa na karbar wannan mukami da kuma warware zare da abawa kan dangantarsa da dan’uwansa, Datti Baba-Ahmed da suke kalubalantar nasarar gwamnatin da ta nada shi mukami har ma da sauran wasu batutuwa. Ga yadda hirar ta kasance:
Da farko masu karatu zasu jin me ya sa ka amince ka amshi mukamin mai taimaka wa mataimakin hugaban kasa a bangaren siyasa?
Toh! Yanzu wanne dan Nijeriya ne bai san halin da kasar take ciki tana bukatar taimako da gudummawa daga wurin duk wani wanda zai iya taimakawa ba?
Da hankalinka da mutuncinka aka ce ka zo ka taimaka mata wajen ceto ta daga cikin halin data ke ciki ka ce ba za ka taimaka ba?
Na zo kamar duk wani dan Nijeriya wanda Allah ya taimaka mishi kuma ya sa shi cikin wadanda suka mori Nijeriya kuma na san yadda kasar ta koma a ce in zo in taimaka kuma na zo na taimaka.
Na gode Allah da ya sa ina cikin wadanda sunansu ya shigo cikin wadanda ake ganin suna da kwarewa da za su iya taimakawa na juya Nijeriya wajen ceto ta daga halin da take ciki da kuma ganin ta koma kasa wacce za ta kasance cikin lumuna da ci gaba wanda jama’arta za su mori abubuwan da alherin da ke cikinta.
Akwai wasu sassa da yawa da ake ganin kana da kwarewa da suka shafi harkokin da za a iya taimaka wa rayuwar al’umma da yawa, amma a ganinka me ya sa suka zabi matsayin mai ba da shawara kan siyasa suka ba ka?
Ai ita siyasa ta kunshi komai saboda na yi aikin gwamnati shekara 28; na koma malamin makaranta kuma ina yin siyasa irin ta jama’a ba ta neman ofis ba. Idan ka harhada irin wadannan duka akwai wanda yake da irin wannan yana gida za a ga idan muka bashi mukami irin na harkokin siyasa zai taimaka mana wajen harhada irin abubuwan da ya yi ko ya iya ko kuma ya kwarance a kai kamar irin nawa da kuma sanin mu’amala na harkokin zamantakewa na Arewa da Nijeriya da gwamnati. Kila abin da da suka gani kenan suka ba ni. Amma ni na san a rayuwa babu abin da babu siyasa kuma mutane sukan yi wani kuskure Sai a ce sai lallai dan siyasa ne za a ba shi aiki na shirya zamantakewar siyasa, ba haka ba ne, wani lokaci ma wanda bai tsaya dumu-dumu cikin siyasa ba ko kuma a ce sai dan jam’iyyar wane ko ba zan yi da wane ba, siyasa ta zama gaba, su ne akan so a kauce ma daga ba su mukamai irin wannan. Amma dai ko ma dai mene ne, ita siyasa rayuwa ce kuma rayuwa mai alheri saboda haka, don an dauko wannan matsayi an bani sai in ce, toh, Ubangiji Allah ya sa shi ya fi alheri kuma na gode.
Daga sanar da wannan matsayi da aka ba ka zuwa yanzu da muke tattaunawa, na san akwai abubuwa da ka fara shirye- shirye a kansu. A ganinka ta wanne bangare ne za ka fara ba da shawara a kai game da rayuwar al’umma, musamma ganin cewa yanzu ne gwamnatin ta hau karagar mulki?
Toh! Na daya dai a halin da suke ciki na shugabanninmu dai ina ganin daya daga cikin abubuwan da zan iya yi wanda zai taimaki al’umma a yanzu shi ne kara tunatar da su halin da kasar nan take ciki. Na san suna da hanyoyi da yawa da za su san irin matsalolin da ‘Yan Nijeriya suke ciki. Daya daga cikin ayyukana da nake ganin zai yi amfani shi ne jaddada musu halin da muke ciki da kuma gyara wadannan matsaloli da muke ciki kamar tsaro, rage talauci da rage rashin aikin yi, da halin da matasanmu suke ciki na lalacewar tarbiyya da harkar ilimi, duk wadannan matsaloline manya wanda kullum ya kamata kana tuna wa shugaba. Na biyu kuma mutane irinmu da suka dauko mu suka ba mu aiki suna da hujjar dauko domin su yi amfani da mu, toh, ya kamata su tambaye mu kai me ka gani, kai me ka gani, kai ka ce kaza, mene ne hujjarka?
Sai a hadu wuri guda a ga ta inda za a yi aiki. Sannan kuma a yi kokari a fito da hanyoyi masu inganci wadanda kuma ba za su dauki lokaci ba wadanda kuma za su rage fitintinu na zamani domin rage halin da ake ciki a Nijeriya da kuma hada kan ‘Yan Nijeriya, dole komai iyawarka sai ka tuntubi mutanen kasa domin samun hanyoyi da za a rage fitintinu da suka shafi kasa. Amma ya danganta da yadda su za su yi amfani da ire-irenmu da suka tare suka ce ku zo ku ba mu shawara.
Akwai wasu ‘Yan Arewa da suke koken cewa shugaba Bola Tinubu ya dauki mukamai masu maiko ya bai wa mutanensu yarbawa. Akwai wadanda suka fara tunkarar ku game da wannan koke kuma kana da shawara da za ka iya ba su gwamnati a kan wannan koken?
Toh! Ka gani dai na yi aiki a gwamnati kusan shekara 28 har babban sakatare na yi na shekara 10. Amfanin abin shi ne kwarewar da mutum yake da ita da kuma rikon amana da mutum zai yi, hakika ba shi da dadi a ce shugaba ya dauki mukamai ya ba nashi kawai. Amma gaskiya na san Tinubu bai ba nashi kawai ba tunda yanzu ga irinmu mun shigo. Na biyu komai iyawarsu akwai ranar da ba kabila za ka kawo ba, aiki ake so, idan an ga aikin nan naka bai gamsar ba canza ka za a yi. Na uku mu sa ido mu gani, shin da wadanda suka fito daga inda shi shugaban kasa ya fito daga sauran wurare shin duka gaba dayanmu ta yaya za mu yi mu taimaka wa wadannan Bayin Allah shi Shugaban Kasa Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima, ta yadda za su fito da Nijeriya daga cikin wannan halin take ciki yanzu. Amma idan mun tsaya muna cewa ga daga inda ya fito, ba wane mukami zai iya kaza, wane zai yi kaza, to ba ma za a duba aikin da suke yi ba sai a kare a fadace-fadace a kan inda suka fito. Shugaban kasa ya san abin da kundin mulkin Nijeriya ya kunsa don ya ce ya bai wa mutum aiki dole ne ya jawo na kusa da shi da kuma dauko na wani wuri saboda haka wadannan mukaman nan da ake ta ta yi suna da yawa yanzu ma aka fara yin su. Ni abin da zance a nan shi ne mu sa ido mu gani inda muka ga ya kamata a gyara sai a gyara. Amma dai abin da nake ganin ya fi muhimmaci shi ne duk wanda za ka dauko ka bashi aiki to ka tabbatar ya cancanci ka ba shi, ba wai kawai don ya fito daga harshe ko addininka ba ne.
Yanzu tun da ka karbi mukamin Mai Bai Wa Mataimakin Shugaban Kasa Shawara A Kan Harkokin Siyasa, yaya matsayin kungiyarka ta dattawan Arewa ta “Northern Elders Forum” shin za ka bar matsayinka ne, kuma ya suka karbi wannan sabon mukamin naka?
Bari in fara da abin da ka tambaya na biyu. Kungiyar Dattawan Arewa ta yaba da wannan matsayi da aka ba ni saboda mun yi taro kuma na gaya musu yadda muka saba na cewa an dauke ni na je mu yi aiki. Kuma mukamina na kakakin Kungiyar Dattawan Arewa za a samu wani a ba shi don aikin ya ci gaba wanda ma kila za a samu wadanda suka fi ni iya aikin. Sannan kuma sun yi murna saboda su dattawa ne domin duk dattijo ya san muhimmaci na a dauko ka, ka zo ka taimaka wa kasa, ka yi aiki, duk wanda aka cewa ka zo ka yi gyara ya ce ba zai yi ba to ya yi laifi. In dai Allah ya ba ka abin da za ka taimaka wa al’umma ka ce ba za ka yi ba to wannan ba dattijo ba ne saboda su dattawa ne sun yi wa Nijeriya aiki, sun yi aiki na kungiyayi domin a taimaka wa Nijeriya saboda haka sun san muhimmacin yin haka kuma sun yaba sosai, akwai takarda ma ta musamman da suka aike wa gwamnati da ta ba ni wannan mukami sannan ni kuma ana min kashedi ka tsaya a kan rikon amana da gaskiya da kyautata wa Arewa. Alhamdu lillahi.
Akwai wadanda suke ganin dan’uwanka yana kotu tare da wannan gwamnati da ka amsa mukami a ciki, sai suke ganin abin ya zama bambarakwai kamar ka kware mishi baya?
Aa, babu wani bambarakwai, ban kware mishi baya ba; yana kotu yana neman hakkinshi kuma mun goyi bayan ya nemi hakkinshi har iya abin da shari’a ta ce a yi. Abin da na je yi ba shi da wata nasaba da neman hakkinshi kuma ya sani, saboda sai da muka zauna muka yi magana da shi kuma ya fahimta, kuma babu wata matsala a ciki. Ni ina cikin gwamnati shi kuma da jam’iyyarshi suna kalubalantar zaben wannan gwamnati a kotu, saboda haka doka ta ba shi dama ya yi haka. Amma ni da shi babu wata matsala.