Bita kan littafin masanin tarihi da al’umma: Zababbun Rubutukan Tarihi na Yusufu Bala Usman, wanda Cibiyar Yusufu Bala Usman ta buga a 2023.
A taron tunawa da cika shekaru 18 da rasuwar Yusufu Bala Usman (1945-2005), Cibiyar Yusufu Bala Usman da ke Zariya ta tattara tare da wallafa tarin takardunsa zuwa littafi. Littafin na dauke da tarin kasidu guda 12 wadanda aka zabo su a tsanake daga mabambantan jigo daga ma’ajin tarihi na Marigay Dakta Bala Usman. Wadannan lakcoci ne da aka gabatar a tarurrukan al’umma, tarurrukan bita da kuma tarukan karawa juna sani, amma sautin su da tsarin su ya yi daidai da ka’idar Bala a matsayin haziki wanda yake fadin gaskiya ga masu mulki. Editocin wannan littafi, George Kwanashe da kuma Norma Perchoneck, sun cancanci yabo saboda hada wadannan kasidu zuwa kundi daya wanda yake dauke da taken: Masanin Tarihi da Al’umma: Zababbun Rubutun Tarihi na Yusufu Bala Usman. Duk da bambance-bambancen jigogi na rubutukansa, amma babukan littafin an tsara su ne bisa tsari a jerin zamani domin bayyana tarihin ra’ayoyin Bala da kuma hanyoyin da “ya yi amfani da su a cikin yanayi daban-daban da kuma batutuwa daban-daban”.
Sunan littafin, ‘The Historian and Society’, ya dace tare da nuna tsattsauran ra’ayi na Bala a matsayinsa na masani kuma dan gwagwarmaya mai fafutuka wanda bayanansa ya zarce iyakokin da aka saba da su na tarihi, ko tsayin da ke bisa tsakanin gari da kuma babbar riga, ko ka’ida da aiki, tare da kuma rashin daidaituwar ra’ayi wanda masana tarihi bisa al’ada suka dankwafa wajen kwatanta tsakanin dauri da yanzu. Kamar yadda Howard Zinn ya lurantar da kyau cewa, “aikin da masana tarihi masu tsattsauran ra’ayi suke yi a cikin dakunan ajiye tarihi da kuma a nau’in rubutunsu shi ne jigon fahimtarsu game da ci gaban jari-hujja da kuma zahirin sadaukarwarsu ga canjin zamantakewar al’umma. Tun da masana tarihin da aka saba da su ba za su tsunduma kansu cikin wannan aiki ba, an bar shi ga masana masu tsattsauran ra’ayi su yi wannan aiki – ta hanyar amfani da ilimi, sadaukarwa, da kuma mutunci- wajen wannan aikin”. Wannan shi ne daidai da yadda Bala ya fahimta kuma ya tunkari aikinsa a matsayinsa na masanin tarihi wanda a koyaushe yake maida bayanai ga masu goyon bayan masu mulki tare da kuma sukar tsarin zalunci. Tare da hangen nesan sa a matsayinsa na masanin tarihi, ayyukan ilimi na Bala ya ba shi damar “sa ilimi a cikin aiki mai kyau domin inganta yanayin dan adam”.
Editocin littafin sun bude littafin da ingantaccen gabatarwa wanda ke zayyana tarihin Bala tare da kwatanta ra’ayoyinsa da ayyukansa a cikin yanayi da lokutan da aka buga su. Tun daga farko, an bai wa mai karatu cikakken fahimtar irin nauyin da ya rataya a wuyan masana tarihi a cikin kasa kamar Nijeriya inda cin hanci da rashawa da siyasar handama da babakere ke ruruwa. Bala ya kasance daya daga cikin hazikai masu azama da bin tsari wadanda ra’ayoyinsu da fahimtarsu suka samo asali daga zuciyarsa. Hakika, wanzuwar ra’ayinsa, daidaiton tsarin nazarinsa, da kuma karfi da zurfin sanin ilmummukansa daban-daban ya bayyana a cikin shafuka 221 na wannan littafin.
Domin fahimtar muhimmancin ra’ayoyinsa da muhawarorinsa da aka gabatar a cikin wannan littafi, yana da gayar muhimmanci ga mai karatu ya gane, a farko, irin gamsassun bayanai da aka kawo cikin rubutukan – da yadda ya nazarci tarihin mulkin mallaka da kuma bambancin wariyar launin fata, bayanan bata suna da kuma munanan ra’ayoyi wadanda aka fassara tarihin Afirka da su a matsayin wani motsi ko dangantaka tsakanin launin fata ko kabilu dake cikin rikici da yaki mara yankewa. Bala ya yi amfani da mafi yawan lokutan ayyukansa ba wai kawai wajen inkarin wannan mummunan fassarar tarihin na wariyar launin fata ba, har ma da bayyana hanyoyin da ba a sani ba wanda aka yi amfani da su a matsayin makamin ‘yan mulkin mallaka da masu rika musu. A don haka mai karatu zai ci karo da baje-kolin hujjoji na ilimi masu karfi wanda ke tabbatar da cewa iko da karfin mulki yana hannun masu karamin karfi ne sabanin abubuwan da aka rika rubutawa a tarihi ana jingina su ga manyan mutane.
Littafin yana dauke da babuka goma sha biyu wanda kowanne babi ya yi bayani mabambanta tare da kawo batutuwa da suka shafi siyasa, tarihi, tattalin arziki, yanayi da kuma sauran su.
Gabadaya, littafin wani bincike ne mai cike da ilmummuka da nazari da kuma tunani game da wasu muhimman jigogi na tarihi, siyasa, tattalin arziki da zamantakewar Nijeriya da ma Afirka wanda aka fitar ta hanyar fahimtar daya daga cikin manyan masana tarihi a nahiyar. Idan ka cire wasu ‘yan kurakurai na rubuce-rubuce, ba wai kawai littafin ya wadatar ga samun bayanai da nazari ba, har ma yana nuni da kyakkyawan dake cikin wajibcin sanin tarihi wajen gina kasa da ci gaban nahiyar Afirka. Daya daga cikin karfin littafin shi ne yadda ya baje kolin bambance-bambancen ilimi da ra’ayuka na tarihi da kuma muhimmancin ra’ayoyi da yawa wajen gina cikakken labari kan kalubalen da Nijeriya ke fuskanta a wannan zamani. Ya kasance a matsayin tunatarwa mai karfi game da nuna dacewar tarihi a matsayin abin da zai saita tunaninmu wajen fahimtar duniya baki daya. Binciken da Bala ya yi a tsanaki, fayyace hujja, da salon rubutu mai kayatarwa ya sa wannan littafin Tarihi ya zama tushe mai kima da kwararrun masana tarihi da masu sha’awar fahimtar ma’anoni da sarkakkiya dake cikin siyasar tattalin arzikin Nijeriya za su yi amfani da shi.
Bisa la’akari da tarin ilimin da aka tanado daga ilmummukan Bala Usman, wanda a halin yanzu yake a cikin Cibiyar Yusufu Bala Usman da ke Zariya, wannan littafi ya zama kamar digon Ba ne. A don haka, bitar da aka gabatar a nan wani mataki ne kawai na abubuwan da ke cikin littafin domin akwai wasu muhimman batutuwa da daman gaske wadanda ma ba a ambace su ba. A karshe ina fatan Cibiyar Yusufu Bala Usman za ta ci gaba da gudanar da aikin da ya kamata na samar da ilmummukan Bala ga al’umma domin amfanin ‘yan Nijeriya da Afirka baki daya.