A wannan makon ne Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta gudanar da babban taronta karo na 78 a Birnin New York da ke kasar Amurka inda shugabannin kasashen duniya daban-daban suka gabatar da jawabai.
A jawabin da ya gabatar ranar Talata da dare ga zauren taron, Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Nahiyar Afirka ta gaji da kashin dankalin da kasashen turawa ke mata, inda ya yi kiran samar da sahihin hadin gwiwa don ci gaban yankin.
Da ya tabo kalubalen Afirka, Shugaban Tinubu ya amince cewa gazawar shugabanci a nahiyar ya kawo cikas ga ci gabanta.
Wannan shi ne jawabinsa na farko a taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a Birnin New York a wannan mako, Tinubu ya kuma yi nuni da irin cikin kashin da Nahiyar Afirka ke samu daga kasashen wajen da suka hada da rashin adalci da cin zarafi.
Ya jaddada cewa wadannan batutuwa na cikin gida sun haifar da cikas ga ci gaban Afirka.
Shugaban Tinubu ya bayyana illar karya alkawuran da aka yi da rashin adalci da cin zarafi, inda ya ce wadannan kalubalen sun yi matukar tasiri da kuma mummunan illa ga ci gaban nahiyar.
Ya yi kira da a yi la’akari da musabbabin kalubalen da na Afirka ta tsinci kanta a ciki.
Tinubu ya yi misali da bayan yakin duniya na biyu lokacin da kasashe suka taru don sake gina al’ummomi, yana nuna bukatar goyon bayan kasashen duniya don ci gaban Afirka, daidai da irin tsarin Marshall.
Ya ce, “Wannan shi ne jawabina na farko a gaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya. Ina so a ni dama in fadi wasu kalmomi a madadin Nijeriya, a madadin Afirka, dangane da taken taron bana.
“Duk da dai an yi jawabai da dama, amma duk da haka matsalolinmu suna kusa da magancewa. Rashin shugabanci nagari ya kawo cikas ga Afirka. Amma karya alkawura, rashin adalci da cin zarafi daga kasashen waje su ma sun haifar da babbar illa ga ci gabanmu.
“Idan aka yi la’akari da dogon tarihin wannan taro, a wannan karon taron zai kasance kasance wani abu na musamman ga Nahiyar Afirka.
“Bayan yakin duniya na biyu, kasashe sun taru a wani yunkuri na sake gina al’ummominsu da yaki ya daidaita. An samar da sabon tsari a duniya kuma an samu babban hadin kai, an kafa Majalisar Dinkin Duniya ne a matsayin wata alama da kuma kariya ga burika da kyawawan akida na Bil’adama.
“Kasashe sun ga cewa bisa amfanin kansu su taimaka wa wasu su fita daga baraguzan gine-gine da wuraren yaki. Taimakon ya yi matukar muhimmanci wanda ya ba kasashe da dama fita daga matsalolin yaki tare da karfafa al’ummomisu.
“Lokacin ya kasance babbar alamar aminici ga cibiyoyin duniya, sannan Dan’adam ya koyi darussan da suka dace wajen samun hadin kai ga duniya baki daya.
“A yau Afirka na neman daukar irin wannan matakin na sadaukar da kai na siyasa da na albarkatun kamar irin shirin Marshall.
“Mun fahimci cewa yanayi da kalubalen tattalin arziki da ke fuskantar Afirka a yau sun sha bamban da na Turai bayan yakin duniya.
“Ba muna neman shirye-shirye iri daya da na ayyuka ba. Abin da muke nema dai shi ne, kokarin hadin gwiwa. Muna neman ingantacciyar hadin gwiwar kasa da kasa da kasashen Afirka don cimma muradin karni na 2030 da kuma muradun ci gaba mai dorewa.”
Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin ganin ci gaban Afirka a matsayin wani abu a duniya. Ya kuma bukataci samar da ayyukan yi da karfafa masana’antu da tabbatar da rarraba harkokin arziki cikin adalci.
Ya tabbatar da cewa mulkin dimokuradiyya na da matukar muhimmanci ga jin dadin al’umma, ya kuma nuna damuwa kan shirye-shiryen siyasa da ke haifar da rashin adalci.