Nijeriya kasa ce matalauciya mai tarin hamshakan masu arziki. Amma ba haka Allah ya tsara ba. Allah ya nufi Nijeriya ta zama kasa mai arziki. Ya ba ta albarkatun ma’adinai masu mahimmanci irin su bakin karfe, kwal, duwatsu masu daraja, danyen mai, yashin gilashi, jan karfe, marmarar kawata gini, gishiri, albarkatun gas, zinare, da dai sauran albarkatun kasa da dama. Yana da matukar wahala a sami wata kasa tilo da ire-ire da yawan wadannan albarkatun ma’adinai a duk fadin duniya.
Nijeriya tana kuma daya daga cikin kasashen da suka fi kasar noma a duniya, wanda hakan ya sa za mu iya noma kusan kowane nau’in amfanin gona, kamar su dankon larabawa, gyada, waken soya, farin wake, masara, kwarar manja, kashu, duk da cewa ba ma fitarwa zuwa kasashen waje walau danyu ko wanda aka sarrafa. An taba yin wani lokaci da Nijeriya ta kasance kasar da ta fi fitar da gyada da koko da kwarar manja zuwa kasashen waje sannan kuma ta yi fice a duniya wajen noman kwakwa da danko da auduga da ‘ya’yan itatuwa dangin lemu da doya, rake da gero da kuma samar da fatu.
- Kasashe 5 Da Nijeriya Ta Fi Shigo Da Kayayyakinsu
- Kungiya Ta Yi Kira Da A Gaggauta Bincike Kan Harin Soji A Kauyen Tudun Biri
Har ila yau, akwai lokacin da muka wadata dukan Yammacin Afirka da kayan masaku.
Har yanzu dai Nijeriya ce kasa mafi yawan arzikin danyen mai a Nahiyar Afirka. Sai dai a makon da ya gabata shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou ya kalli tsabar idanunmu da wasu kasashe da ke saurarensa, ya fadi cewa kasarsa Jamhuriyar Nijar, daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya, ba da jimawa ba za ta fara fitar da albarkatun man fetur zuwa Nijeriya.
’Yan Nijeriya ba su yi fushi ba a zahiri. Saboda tsananin bacin rai suka yi gum da bakinsu. Nijeriya ita ce kasa ta 12 cikin kasashe mafiya arzikin man fetur a duniya sannan kuma kasa ta takwas wajen fitar da mai sannan ita ce take da katafaran ma’ajiyar mai na 10 mafi girma a duniya. Shugaban Jamhuriyar Nijar ya ce za a fara wannan abin kunya (ga kasarmu) ne daga watan Disamba na wannan shekara, saboda kusan sun kammala aikin gina matatar mai ta Zinder. Jamhuriyar Nijar za ta sayi danyen manmu, ta tace sannan ta sake sayar da shi ga jihohin arewacin Nijeriya.
Kudaden da Nijeriya ta samu daga sayar da danyen man fetur a shekarun mulkin Obasanjo tsakanin 1999 zuwa 2007 ya fi karfin hankali. A daidai lokacin ne farashin danyen mai a kasashen duniya ya kai dalar Amurka 147 kowace ganga, wanda ba a taba ganin irinsa ba, kuma wani abu mafi kyau a lokacin, farashin bai taba yin kasa da dala 120 kan kowacce ganga ba. Sakamakon haka, Gwamnatin Obasanjo ta samu kudaden shiga fiye da duk wanda gwamnatocin Tafawa Balewa, Aguiyi Ironsi, Yakubu Gowon, Murtala Mohammed, Gwamnatin Obasanjon ta soja, Shehu Shagari, Muhammadu Buhari, Ibrahim Babangida, Sani Abacha da Abdulsalami Abubakar, suka samu idan aka hada baki daya.
Amma duk da haka, Obasanjo bai gina matatar mai ko daya ba kuma bai gyara matatun mai hudu da ya zo ya tarar da su ba. Bai gina sabbin tashoshin jiragen ruwa da filayen jiragen sama ba kuma bai gyara tsoffin da ya tarar da su ba. Obasanjo ya kashe Kamfanin Jirage na Kasa (Nigeria Airways), a maimakon haka ya sayi sabbin jiragen sama ga fadar shugaban kasa da ya alakanta da ofishinsa.
A yau, idan ka zagaya filayen jiragen sama na duniya, za ka ga jirage mallakin kamfanonin kasashe irin su Ghana, Kenya, Afirka ta Kudu, Habasha, Masar, Koriya, Maleshiya, Indonesiya, Singapor, da dai sauransu, idan ka tsame na Afirka ta Kudu, duk wadannan kamfanonin jiragen na kasashen da a baya suka fi Nijeriya tsananin talauci ne.
Har ila yau, an shaida mana cewa kasar Chadi, daya daga cikin matalautan kasashe makwabta, ta daina shigo da man fetur cikin kasarta, saboda ta dogara da kanta wajen tace man fetur a cikin gida. Nan ba da jimawa ba su ma za su fara tunanin fitar da man fetur zuwa Nijeriya. Lokacin da Obasanjo ya hau karaga a 1999, ya yi alkawarin samar da wutar lantarki megawatt 10,000 zuwa shekarar 2007. Amma a karshen makon da ya gabata, ministan wutar lantarki, Farfesa Barth Nnaji, ya sha alwashin kara yawan wutar daga megawatts 4,200 zuwa megawatt 5,000 a watan Disamba.
Satar kudin Nijeriya da irin muguwar almundahanar da muka gani a zamanin mulkin Obasanjo sun dara na gwamnatocin da suka gabace shi. Ta’azzarar cin hanci da rashawa saboda rashin iya shugabancin gwamnatinsa suka tsunduma Nijeriya a wannan hali.
Halin da muke ciki ya kara dagulewa ganin yadda shugabancin kasar nan ya nuna rashin sanin makamar aiki wajen warware matsalar tsaron kasar. Nijeriya ta yi suna a bangaren yawaitar aikata laifuka. Mutane da yawa sun manta cewa mallakar bindigogi ba tare da lasisi ba babban laifi ne.
A kullum ana samun rahotannin garkuwa da mutane musamman a Kudu maso Gabas da Kudu-maso-Kudu, da ayyukan soji a yankin Neja-Delta, barnar Boko Haram a yankin Arewacin kasar nan, da ta’azzarar kiyayya saboda kabilanci da bambancin addini a Nijeriya, da kuma kashe-kashen siyasa a fadin kasar. Gwamnati ba ta hankalta ba kuma ta rasa mafita inda ta bar ‘yan Nijeriya kowa ya yi ta kansa. Bayan harin bam da aka kai harabar hedkwatar Rundunar ‘Yansandan Nijeriya da ke Abuja a kwanan baya, abin da shugaban kasa ya iya fada mana shi ne, shi ma ‘yan Boko Haram na neman sa, kuma idan sun same shi za su jefa masa bam. A takaice dai abin da ake nufi shi ne, kowa tasa ta fishe shi.
A duk duniya, Nijeriya ta yi kaurin suna da laifukan damfara na 419. Masu aikata laifukan Nijeriya ma suna da hannu a wasu ayyukan ‘yan fashin teku musamman a yankunan da ake hako mai. Tsakanin watan Janairun 2007 zuwa Oktobar 2007, an sami rahotannin hare-haren ‘yan fashin teku 26. Gwamnatoci a Nijeriya tun daga Gwamnatin Obasanjo, ba su nuna wata kwarewa wajen kare mutunci, rayuka da dukiyoyin ’yan Nijeriya masu bin doka da oda ba daga masu aikata laifukan da suke cin karensu ba babbaka, domin sun san ba za a kama su ba.
Gaskiyar magana mai daci game da Nijeriya ita ce, za mu ci gaba da samun koma-baya, daga bisani kuma mu shiga sahun kasashe irin su Somaliya, har sai mun fara tabbatar da cewa mutanen da suka kware masu himma wajen ciyar da Nijeriya gaba, da za su yi tsayin daka wajen yakar cin hanci da rashawa ne kawai aka zaba a matsayin shugabanni. Tsarin samar da shugabanni a Nijeriya da ake amfani da shi zai ci gaba da haifar da rashin ci gabanmu.
Kasashen da ko kamshin Nijeriya ba su ji ba wajen ci gaba a shekarun 1960 da 1970 irin su Koriya ta Kudu, Indonesiya, Malesiya, da Singapore a yanzu sun yi mana nisa ta fuskar ci gaba da zamanantar kasashensu.
A cikin shekarun 1970, Indiyawa da Sinawa sun rika tururuwar zuwa Nijeriya don samun aikin yi. A yau, ‘yan Nijeriya suna fitar farin dango zuwa Indiya don neman lafiya a asibitocinsu, Singapore na da karancin albarkatun kasa da ya sa hatta ruwan sha mai tsafta ba ta da shi. Ta dogara ce da Malesiya don samun ruwan sha. A yau, Singapore kasa ce mai arzikin man fetur, duk da cewa ba ta samar da ko da digo na mai.
Matatun mai daban-daban na kasar Singapore suna tace sama da ganga miliyan biyu na mai a kullum (kimanin yadda muke hakowa yanzu a kullum) daga danyen man da take shigo da shi daga kasashe kamar Nijeriya. Malesiya tana hako kusan ganga 700,000 na mai a duk rana, idan aka kwatanta da ganga miliyan 2.6 da Nijeriya ke hakowa a kullum, amma duk da haka, akwai lokacin da katafaren tagwayen ginin Petronas Twin Towers da ke Kuala Lumpur, babban birnin Malesiya, ya kasance gini mafi tsawo a duniya wanda alama ce da ke nuna karfin tattalin arzikin kasar da kuma bunkasarta. Petronas na Malesiya kwatankwacin kamfaninmu na NNPC yake.
A cikin shekarun 1970, ‘yan kasar Malesiya sun sace ‘yan kwarorin irin shuka na kwarar manja daga gare mu saboda ba su da su. A shekara ta 2008, Malesiya tana samar da ton miliyan 7.7 na kwarar manja daga kadadar gona miliyan 4,500,000, wanda hakan ya sa ta zama kasa ta biyu wajen samar da kwarar manja a duniya.
Ban da haka ma, sana’ar kwarar manja tana samar da ayyukan yi na kai-tsaye kusan 600,000, wanda hakan ya sa mutanen kasar suna samun aikin yi tare da rage aikata laifuka.
Ita da dai Malesiya wacce ta samu irin shuka daga wurinmu, yanzu tana kawo mana manja mu saya. Kudin shigar da take samu daga kwarar manja ya zarce na danyen mai. Malesiya ta yi fintikau a noman kwarar manja kafin Indonesiya ta sha gabanta a shekarar 2006 inda ta zama kasa ta farko a duniya wajen samar da kwarar manja duk da cewa, ita ba kamar Malesiya ba, galibin abin da take fitarwa waje danyen manjan ne ba wanda aka sarrafa ba.
Ka da mu manta cewa asalin kwarar manjar nan ba daga wadannan kasashen ne ba. Kyakkyawan shugabanci a wadannan kasashe shi ne babbar silar samun wannan arziki da albarka. Asalin kwarar manja daga Yammacin Afirka ne kuma akwai lokacin da Nijeriya ta kasance kan gaba wajen nomawa a duniya.
Zan diga ayar wannan mukala a yau da abin da na saba fada, na sha nanatawa. Matukar ba mu samu matsaya daya a tsakanin manyan kasa kan tsarin samar da shugabanni a kasar nan ba, muka ci gaba da kyale gungun ‘yan bindiga suna cin karensu ba babbaka wajen sace-sacen zabe da dora kansu a kanmu ta hanyar magudin zabe, to ba wai kawai kasashe irin su Malesiya, Taiwan, Singapore, Koriya ta Kudu ne za su ci gaba da tsere mana ba, Jamhuriyar Nijar da Chadi ma za su yi mana fintikau. Wace shaida ce muke bukata cewa hakan ba za ta faru ba? Ashe ba mu fara shigo da man fetur daga gare su ba?
An wallafa wannan mukala a karon farko a shafin Sam, mai taken Babbar Magana, cikin Agustan 2011. An sake wallafawa ne domin tunawa da shi a ranar Litinin da ta gabata, lokacin da ya cika shekara uku da rasuwa.