Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya bayyana rashin shugabanci nagari a matsayin dalilin da ya sa ‘yan Nijeriya ba su iya cin moriyar dimokuradiyya ba tun bayan dawowar mulkin farar hula na tsawon shekaru 23.
Jega ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da kasida a wurin taron Cibiyar Nazarin Ayyukan Majalisun Dokoki da Dimokuradiyya ta Kasa (NILDS) da ta shirya a Ilorin, Jihar Kwara. Ya ce Nijeriya ta fara fuskantar mummunan shugabanci ne tun bayan dawowar gwamnatin farar hula.
- Yau Kotu Za Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da Emefiele Ya Shigar
- Tinubu Ya Ba Da Umarnin Fitar Da Takin Zamani Da Hatsi Don Rage Radadin Cire Tallafin Fetur
Yayin da yake korafin cewa duk da cewa Nijeriya ta yi shugabanni daban-daban a mulkin farar hula, amma kasar na cikin mawuyacin hali na rashin shugabanni nagari.
Ya ce, “Nijeriya ta kasance a kan turbar ci gaban dimokuradiyya mai sassaucin ra’ayi har tsawon shekaru 23, tun daga shekarar 1999 da sojoji suka mika mulki ga fararen hula, duk shekara hudu muna zabar wakilai a majalisun dokoki da na zartaswa na gwamnati, wadannan abubuwa na ci gaban dimokuradiyya ne masu sassaucin ra’ayi wanda har yanzu ba su juya zuwa ingantacce ba wanda zai gamsar da bukatar al’ummar kasar nan.
“Shekaru 23 da suka gabata, kasar nan tana karkashin mulkin dimokuradiyya, amma har yanzu abin da ake kira rabon dimokuradiyya bai kasance abin sha’awa ga yawancin ‘yan Nijeriya ba. Sai dai kash, an samu shugabanci mara kyau, ba wai babu shugabanni nagari a kasar ba, amma sun yi karanci, yayin da cibiyoyin dimokuradiyya suka kasance masu rauni.
“Gaba daya shugabanci a kowane mataki na tarayyar Nijeriya bai da kyau, ya kasance mummuna da rashin bin tsarin dimokuradiyya, maimakon ya kasance mai kyau ta hanyar tafarkin mulkin dimokuradiyya.
“Mafi yawancin kungiyoyi da cibiyoyi da na kasar nan suma sun harbu da rashin shugabanci nagari.