Yayin da aka cika shekaru 25 da dawowar yankin Hong Kong kasar Sin, firaministan kasar Birtaniya Boris Johnson da jami’in kula da harkokin waje da raya kasa na kasar Liz Truss sun ba da jawabi da sanarwa cewa, Birtaniya tana da alhakin kula da mazaunen yankin Hong Kong bisa hadaddiyar sanarwa a tsakanin Sin da Birtaniya, dake nuna cewa Birtaniya ba ta yi watsi da yankin Hong Kong ba.
Wannan batun siyasa abin dariya ne, wanda ya shaida cewa, tsoffin ‘yan mulkin mallaka ba su son amincewa da hakikanin yanayi na yanzu, wato ba su da karfi kamar yadda suke da shi a lokacin baya, suna yunkurin tsoma baki a harkokin yankin Hong Kong, har ma harkokin cikin gida na kasar Sin.
Gwamnatocin Sin da Birtaniya sun daddale hadaddiyar sanarwa a tsakaninsu a watan Disamba na shekarar 1984, don daidaita batun dawowar yankin Hong Kong kasar Sin, abu mafi muhimmanci shi ne Sin ta maido da ikon mulkin kasa a yankin.
Bisa sanarwar, bayan da aka dawo da yankin Hong Kong a kasar Sin a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1997, kasar Birtaniya ba ta da ikon mulkin yankin da ikon tafiyar da harkokin yankin da kuma ikon sa ido kan yankin. Wato kasar Birtaniya ba ta da ikon tsoma baki a harkokin yankin na Hong Kong.
Akwai shaidu da dama dake bayyana yankin Hong Kong na samu ci gaba ko a’a, kamar irin yadda yankin ya zama yankin tattalin arziki mafi ‘yanci a duniya, da cibiyar hada-hadar kudi ta duniya, da cibiyar zirga-zirgar jiragen ruwa ta duniya, da kuma cibiyar yin ciniki ta duniya da sauransu.
A cikin shekaru 25 bayan dawowar yankin, an samu manyan nasarori a yankin, kana an aiwatar da manufar “kasa daya amma tsarin mulki biyu” a yankin cikin nasara.
A kasar Birtaniya kuwa, Scotland tana kokarin neman ‘yancin kai ta hanyar jin ra’ayoyin jama’a. Kana Ireland ta Arewa ita ma tana son ballewa daga Birtaniya. A lokacin, firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce, ba zai yi watsi da yankin Hong Kong ba, yunkurinsa shi ne nuna karfi ga waje da yin magana a duniya don sassauta matsalolin cikin kasar, yunkurin zai ci tura.
Yankin Hong Kong yanki ne na kasar Sin, ba shi da nasaba da kasar Birtaniya. (Zainab)