Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana zaben 2023 a matsayin wata dama ta musamman ga yankin Kudu maso Gabas.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron jam’iyyar a jihar Gombe a ranar Asabar, Kwankwaso ya ce yankin Kudu maso Gabas na da kwarewa a harkar kasuwanci kuma mutanen yankin suna da basira, amma “ya kamata su koyi siyasa… a bangaren siyasa, su ne koma baya.” inji Daily trust
Ya bayyana cewa ‘yan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC da PDP duk ba wanda ya dauki Mataimaki daga Yankin Kudu Maso gabas, don haka wannan dama ce da ya dace yankin ya bi jam’iyyar NNPP a dama da su.
Ya bayyana cewa masu cewa “ko da abokina (Peter Obi) yana son zama mataimakina a takarar shugaban kasa, wasu mutanen Kudu maso Gabas ba za su yarda ba, wannan ba dabara ba ce.”
Kwankwaso ya bada misalin jigo kuma dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmad Tinubu, inda ya ce Mutum ne mai dabara, ya goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015, “yau shi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.”
Kwankwaso ya ce zabin da ya fi dacewa da yankin Kudu maso Gabas shi ne hadin gwiwar shiyyar da NNPP, “wannan wata dama ce ta musamman, idan suka rasa ta, shiyyar tana cikin babban kalubale.”