Ranar Talata 4 ga watan Fabrairu da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa biyu Athletico Madrid da Getafe zasu kece raini a filin wasa na wanda Metropolitano dake birnin Madrid, domin neman gurbin tikitin wasan na kusa da na ƙarshe na gasar Copa Del Rey da ake bugawa a ƙasar Sifaniya.
Atletico Madrid za ta yi niyyar samun gurbin zuwa wasan kusa da na ƙarshe na gasar Copa del Rey lokacin da za su yi maraba da abokan hamayyar La Liga Getafe a filin wasa na wanda Metropolitano a daren Talata.
- Shin Barcelona Da Atletico Madrid Zu Su Iya Dakatar Da Real Madrid A La Liga?
- Athletico Madrid Ta Buga Canjaras Da Real Sociedad A Wasan Sada Zumunci
Tawagar Diego Simeone za ta shiga fafatawar ne bayan nasarar da ta samu a kan Mallorca da ci 2-0 a gasar ta Sifaniya, yayin da ita ma Getafe ke ji da kanta bayan ta buga canjaras da Sevilla a ƙarshen makon da ya gabata, Atletico na ci gaba da jan zarenta a fagen ƙwallon ƙafa ta bana.
In da ƙungiyar da Diego Simeone ke jagoranta ta tsallake zuwa zagayen gaba na gasar zakarun Turai, yayin da take matsayi na biyu a teburin La Liga, maki ɗaya kacal tsakaninta da Real Madrid, haka zalika za su je Bernabeu a ƙarshen mako mai zuwa domin tunkarar Real Madrid, idan ta samu nasara akan masu riƙe da kofin na Laliga zasu koma matsayi na ɗaya akan teburin gasar.
Getafe ba ta taɓa lashe kofin Copa del Rey ba, amma sau biyu a baya ta kasance a wasan ƙarshe a shekarun 2007 da 2008, amma kuma Getafe ta doke Manises, da Orihuela, da Granada da Pontevedra a wasannin da ta buga a gasar ta bana, wannan shi ne karon farko da ƙungiyoyin biyu suka kara a gasar Copa del Rey tun watan Janairun shekarar 2013, inda ƙungiyoyin biyu suka tashi 0-0.
Mai yiwuwa Atletico Madrid za ta fara wasa da wannan zubin:
Musso, Llorente, Gimenez, Witsel, Azpilicueta, Correa, Gallagher, Koke, Lino, Sorloth, Griezmann.
Mai yiwuwa Getafe zata fara da wannan zubin:
Letacek, Iglesias, Duarte, Alderete, Rico, Alena, Dakonam, Arambarri, Sola, Uche, Mayoral.