Babban filin wasa na ƙasar Ingila Wembley Stadium da ke birnin Landan shi zai karɓi baƙuncin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar a yau Asabar inda za’a buga wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai na wannan shekarar.
Wasan wanda zai gudana a tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid wadda ta lashe kofin Laliga a bana da kuma abokiyar karawarta Borrusia Dortmund ta ƙasar Jamus, ana tsammanin zai kasance wasa mai ƙayatarwa duba da cewa dukkan ƙungiyoyin biyu ba abin rainawa ba ne a fagen ƙwallon ƙafa a Duniya.
- Za A Fara Bayar Da Shudin Kati A Kwallon Kafa
- Makarantar Horas Da ‘Yan Kwallo Ta Katsina Zata Wakilci Nijeriya A Gasar Kofin Dana Na Denmark
Real Madrid da Borrusia Dortmund sun haɗu sau 14 a tsakaninsu a mabanbantan kofuna da lokuta, inda Real Madrid take kan gaba a samun nasarori a dukkan wasannin da suka haɗu da Dortmund.
Wasa na ƙarshe da Dortmund ta doke Real Madrid shi ne wasan da suka buga a filin wasa na Signal Iduna Park a wasa na kusa da na ƙarshe a shekarar 2014 inda kyaftin ɗin Dortmund Marco Reus ya jefa dukkan kwallaye biyun da Dortmund ta ci a wasan.
A karawa 14 Real Madrid ta samu nasara sau 6 an yi canjaras 5 sai kuma Dortmund ta doke su sau 3. Wannan wasa da za’a buga yau zai matuƙar ɗaukar hankalin masu sha’awar kallon ƙwallon ƙafa a faɗin Duniya.