Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya kare kansa kan zaben Sanata Kashim Shettima (Musulmi) a matsayin abokin takararsa a 2023.
Kafin Zabar Shettima, siyasar Tinubu ta sha suka daban-daban kan yunkurin tsayar da Musulmi abokin takararsa.
Kungiyar kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta yi watsi da kudurin dan takarar tare da gargadin jam’iyyu game da hakan, sai dai wasu masu ruwa da tsaki sun bukaci ‘yan Nijeriya da su mai da hankali kan cancanta fiye da Lura da addini ko al’adda ko shiyyar da dan takara ya fito.
Da yake kare kansa kan zabar Shettima a matsayin abokin takararsa, Tinubu ya ce duk rayuwarsa, ta kare ne wajen bin ka’idojin cancanta ga abokan dake kewaye da shi, wadanda ke da kwarewa, basira da sanin ya kamata.
Tinubu ya kara da cewa, “Na nemi shawarwari sosai kan batun mataimakina, na ji dadin ra’ayoyin manya ‘ya’yan jam’iyyarmu da abokan siyasa da manyan jiga-jigan kasa, wadanda ke kishin makomar Nijeriya kamar yadda nake yi”.