Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, a karshen mako ya bayyana cewa matatar man Dangote ta ci gaba da karbar bukatun sayen kayayyakin da take tacewa akai-akai daga duk wadanda suka sayi kayayyakin tun da aka fara aikin tace man. Kawo yanzu dai matatar ta fitar da kayayyakinta zuwa wasu kasashen Turai, Singapore da kuma gabar tekun Lome.
Da yake jawabi a yayin rangadin da ‘yan majalisar wakilai suka kai wa kamfanin mai da taki na Dangote, ya yi mamakin dalilin da ya sa hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya, NMDPRA, wacce ya kamata ta kare masana’antu na cikin gida, amma ta yi zargin batanci ga Matatar. Abun mamaki ma shi ne karya a rahotannin kafafen yada labarai don ci gaba da shigo da gurbataccen man fetur cikin Nijeriya.
- Kalaman Batanci Akan Matatatar Man Fetur Ta Dangote Barazana Ce Ga Nijeriya Da Afirka – Masani
- Zanga-Zanga: Ba A Gyara Barna Da Barna
A cewarsa: “Ina kira gare ku da ku kafa kwamitin da zai dauki samfuran Man mu domin gwaji. Ta yin haka, za ku iya gaya wa ’yan Nijeriya ainihin gaskiyar da suka cancanci su sani.
“Na yi matukar farin ciki da yadda kuka nemi a yi gwaji. kuma na tabbata kun gigice da sakamakon da kuka samu. Da sakamakon haka, za ku ga mun samar da dizal mafi inganci a Nijeriya.”
Dangote ya fito karara ya kalubalanci hukumar (NMDPRA) da ta kwatanta ingancin kayan da ake tacewa daga matatar man fetur da ake shigo da su daga kasashen waje, yayin da ya yi kira da a tantance ba tare da nuna son kai ba domin sanin abin da zai dace da muradun ‘yan Nijeriya.