Zababbun mambobin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, sun amince da sake zabar Honarabul Abubakar Y. Sulaiman a matsayin kakakin Majalisar ta 10.
Sulaiman, ya samu nasarar zarcewa ne babu hamayya a zaben da aka gudanar a ranar Talata 20 ga watan Yunin 2023 biyo bayan kaddamar da majalisar ta 10.
- Tinubu Zai Hallarci Taron Kolin Tattalin Arziki A Paris
- An Bai Wa Iyalin ‘Yansandan Da Suka Mutu A Bakin Aiki Cakin 23m A Zamfara
Akawun majalisar Dokokin Jihar, Umar Yusuf Gital ne, ya jagoranci kaddamar da majalisar.
Zababben dan majalisar da ke wakiltar Jama’are, Honarabul Mubarak Haruna (daga NNPP) ne, ya gabatar da bukatar zabar Abubakar a matsayin kakakin sai kuma Honarabul Auwal Hassan daga mazabar Shira ya mara masa baya.
Abubakar Y. Sulaiman da ke wakiltar mazabar Ningi dai mamban jam’iyyar PDP ne, wanda ya jagoranci majalisar Dokokin Jihar ta 9 yanzu kuma zai jagoranci ta 10.
Kazalika, zabbabbun ‘yan majalisar sun kuma zabi Honarabul Jamilu Umar Dahiru (mamban PDP da ke wakiltar mazabar cikin Bauchi) a matsayin mataimakin shugaban majalisar Dokokin Jihar ta 10.
Habibu Umar Esq daga mazabar Kirfi ne tashi domin gabatar da Jamilu a matsayin mataimakin shugaban majalisar da ya samu marawar baya ga Honarabul Bello Jadauri daga mazabar Gamawa.
Tuni aka rantsar da su domin kama aiki a matsayin jagororin majalisar dokokin ta jihar Bauchi.